Ganduje ne ya baiwa NLC kudi sukai Zanga-zanga a Kaduna-El-Rufa’i.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El Rufa’i ya zargi gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da daukar nauyin kungiyar kwadago NLC don Yi Masa Yajin aiki da Zanga-zanga.

Cikin wani faifan audio dake yawo a kafafen sada Zumunta an jiyo Gwamna Nasir El Rufa’i na zargin da hadin bakin gwamnan Kano akan Waccen tirjiya daya fuskanta daga gamayyar kungiyoyin kwadago.

“Gwamnan Kano Ganduje ne ya baiwa Yan Kungiyar Kwadago kudi domin su yi Zanga-zanga a jihar Kaduna”Inji El-Rufa’i Cikin harshen Turanci.

Gwamnatin jihar Kano dai batace uffan ba kan wannan zargi, sai dai masu lura da al’amura na ganin cewa gwamnan na Kaduna ya girbi abinda ya shuka ne na korar ma’aikatan jihar tare da kin yadda asamu maslaha da kungiyoyin na kwadago.

A makon daya karene kungiyar kwadago ta NLC da sauran takwarorinta suka shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar sakamakon kin amincewa da matakin gwamnan na Kaduna na korar ma’aikata fiyeda dubu biyu lamarin daya tsayar da jihar cak ta fannoni tattalin arziki da zamantakewa.

To Sai dai a rana ta biyu ta yajin aikin, Gwamna El Rufa’i ya sake korar ma’aikatan lafiya na jihar daga matakin albashi na 14 zuwa kasa.

Ana dai cigaba da sulhuntawa tsakanin gwamnatin jihar kadunan da kungiyar kwadago karkashin shiga tsakanin ministan kwadago da nagartar aiki Dr Chris Ngige.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here