Advert
Home Sashen Hausa GANAWAR SIRRI TSAKANIN 'YAN MAJALISA DA KANTOMAN RIKO NA APC A JAHAR...

GANAWAR SIRRI TSAKANIN ‘YAN MAJALISA DA KANTOMAN RIKO NA APC A JAHAR KATSINA

GANAWAR SIRRI TSAKANIN ‘YAN MAJALISA DA KANTOMAN RIKO NA APC A JAHAR KATSINA

Suleman Chiroma
@ Jaridar Taskar Labarai

A cikin makon nan ne Kakakin Majalisar dokokin Jihar Katsina, hon tasi u isah maigari ya jagoranci kusan duk ‘yan Majalisar dokokin zuwa gidan Kantoman riko na jam’iyyar APC, Ustaz Shitu S. Shitu, inda suka yi wata ganawar sirri.
Me ya Sanya a gida ba ofis na majalisa ko na gidan gwamnati ba ko ofishin jam iyya shine abin da ake ta cece ku ce duk katsina

A lokacin ganawar, wadda sama da ‘yan Majalisar dokokin Jihar Katsina 20 na ciki, an kulle kofa, an kuma sallami kowa, daga ‘yan Majalisar, sai Kantoman, sai kuma wani mataimakinsa.

Majiyarmu ta tabbatar wa da jaridar nan cewa an dau tsawon lokaci ana ganawar, daga baya aka bude kofa aka fito ‘yan Majalisar suka kama gabansu.

Babban abin da ya daure wa mutane kai shi ne, ‘yan Majalisar Wakilan jama’a a ne, amma sam sun ki bayyana wa al’ummarsu wane sirri aka tattauna.

Lokacin da labarin ya fara yawo, wasu sun tuntubi ‘yan Majalisarsu don jin abin da aka tattauna, amma sun ki fada masu.

Jaridar nan ta samu tabbacin hakan daga Kananan Hukumomi tara. Me ake boyewa ne?

Jaridar nan ta kuma samu tabbacin har zuwa rubuta rahoton nan Kantoman riko na jam’iyyar bai kira taron sauran shugabannin jam’iyyar ba na Jiha da Kananan Hukumomi ya bayyana masu sirrin da aka kulla tsakaninsa da wadancan ‘yan Majalisun ba, duk kuwa da jam’iyya ta ‘ya’yanta ce, kuma ta kowa ce.

Tambayar da ke ta yawo a Katsina ita ce, yaushe ‘yan Majalisun Jihar Wakilan al’umma da aka zaba da Kantoman riko na jam’iyyar na Jihar suka fara tafiyar da Jihar a sirrance ba sa bukatar a san me suka kitsa bayan sun kulle daki?

Da aka rutsa wani Dan Majalisar wata Karamar Hukuma don ya bayyana wa al’ummarsa me aka tattauna. Ya ce sai da aka sa suka rantse ba za su fada wa kowa ba kafin a fara taron, don haka ya halarta. Ya ce abin da aka tattauna su yi hakuri ba za su ji ba don kar rantsuwa ta ci shi.

Wa ya ya fi laifi a tsakaninsu? Wasu na ganin ‘yan Majalisun, don sune Wakilan da aka zaba suka nemi kuri’a suka yi rantsuwa da Alkur’ani.

Binciken jaridar nan ya tabbatar Kantoman rikon jam’iyyar, Ustaz Shitu S. Shitu, wasu na ganin tuntuni aka dawo daga rakiyaarsa, domin shi ne ke amfana da jam’iyyar fiye da kishinta a kan jama’a.

Kazalika shi ne Shugaban jam’iyya da ya samu kudi fiye da kowane da aka taba yi a tarihin Jihar Katsina, kamar yadda binciken da jaridar Taskar Labarai ta taba bugawa ya tabbatar.

Kuma shi ne wanda ke rayuwar Sarakunan Larabawa, amma shugabannin jam’iyyar na Kananan Hukumomi da Mazabu da wasu a Jiha suna rayuwar kyankyason masallaci.

Shi ne wanda Hukumar Kwastam ta dora wa haraji a kan zargin da kwastam suka ce an aikata ba daidai ba, amma Hukumar ana ganin tana daga masa kafa don yana Shugaban jam’iyyar Jihar Shugaban kasa, kamar yadda wata takarda da jaridar Taskar Labarai ta gani ya tabbatar da hakan.

Binciken jaridar nan ya tabbatar Kantoman rikon ya mayar da jam’iyyar jari, kuma garkuwa, fiye da kishinta ko mabiyanta, don haka ko mai ya yi babu mamaki.

Ra’ayoyi da jaridar nan ta samu, shi ne ‘yan Majalisar da suka gana su yi Azumi su karya rantsuwar da suka yi su bayyana wa al’ummar Katsina gaskiyar me suka tattauna a wancan ganawar sirrin, kuma su fadi tsakaninsu da Allah.

Wannan shi ne muryoyin da jaridar Taskar Labarai ta jiyo suna amo.

Jaridar nan ta tuntubi Kakakin jami’iyyar, Abu Gambo Dan Musa ta lambarsa (08037053560), amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba. Mun aika masa sakon rubutu, ba amsa.

Mun tuntubi Kantoman rikon na jam’iyyar, Ustaz Shitu S. Shitu ta waya bai dauki kiran ba, mun aika masa sakon rubutu bai mai do amsa ba.
________________________
Jaridar Taskar Labarai na bisa yanar gizo a shafin www.taskarlabarai.com. da sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo. Tana da ‘yar’uwa mai suna Katsina City News da ke a www.katsinacitynews.com da kuma The Links News da ke www.thelinksnews.com. Duk wani sako a aika ga 07043777779 ko katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Yanda aikin samar da Ruwan Sha, yake gudana a cikin Birnin Katsina… Gwamna Amin Bello Masari ya zagaya

A ci gaba da aikin gyaran ruwan cikin birnin Katsina da kewaye, a yau, Gwamna Aminu Bello Masari ya zagaya wuraren da muhimman ayyukan...

MU NA GAB DA AIWATAR DA ZABUKAN KANANAN HUKUMOMI, ZAKUMA MU SAMAR DA YANAYIN DA MANOMA ZA SU YI NOMA CIKIN NATSUWA

Gwamna Aminu Bello Masari ya bada tabbacin cewa Gwamnatin Jiha, hadin guiwa da jami'an tsaro da kuma masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron,...

HOTO: Gwarazan Kokowa na ƙasar Nijar

Gwarzaye abin alfaharin NIGER 🇳🇪 Kamar yadda Kwallon yayi fice a Brazil, Kamar yadda Criquet yayi fice a India, Kamar yadda NBA yayi fice a USA, Kamar yadda...

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina tayi Nasarar chafke Barayin Babura…..

Rundunar ta bayyana yadda tayi Nasarar chafke Barayin masu fasa Gidajen Mutane suna satar masu Babura, a ranar 6/6/2021, bisa ga Rahotannin sirri rundunar...

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA….

KOWA YA KARE KANSHI DAGA HARIN YAN BINDIGA....inji gwamnan zamfara Daga Hussaini Ibrahim, Gusau @ katsina city news A cigaban da bukikuwan cika shekaru biyu da Gwamnatin...
%d bloggers like this: