Advert
Home Sashen Hausa GAMAYYAR KUNGIYAR FARAR HULA A JAHAR KATSINA TAYI KIRA DA A DAKATAR...

GAMAYYAR KUNGIYAR FARAR HULA A JAHAR KATSINA TAYI KIRA DA A DAKATAR DA MUKADDASHIN SHUGABAN JAMI’AR UMYU

GAMAYYAR KUNGIYAR FARAR HULA A JAHAR KATSINA TAYI KIRA DA A DAKATAR DA MUKADDASHIN SHUGABAN JAMI’AR UMYU

Hassan Male @Katsina City News 🗞️

Gamayyar Kungiyar farar hula ta jahar Katsina tayi kira ga kwamitin bincike da babbar majalisar zartaswa ta jami’ar Ummaru Musa Yar’adua ta kafa da ya gaggauta dakatar da mukaddashin shugaban jami’ar biyo bayan rahoton zargin aikata ba dai dai ba a kansa.

In za a iya tunawa, sunan Farfesa Sanusi Mamman a yan’ kwanakin nan ya bazu a kafafen sadarwa na zamani biyo bayan zargin yin mummunar alaqa da wata daliba a jami’ar.

A wata takardar manema labarai da shugaban Kungiyar AbdurRahman Abdullahi ya sanyawa hannu, Kungiyar ta nuna cewar madamar ana so a tabbatar da gaskiya da adalci a binciken da akeyi, to dole sai an dakatar da Sanusi Mamman daga kan mukamin sa har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

Kamar yadda Kungiyar ta sanar, barin shugaban jami’ar kan mukamin sa ka iya haifar da canzawa, ko kirkirar sababbin bayanai tare da rashin samun damar Isa ga bayanan da ake da bukatar samu ko kuma jefa wasu mutanen da ake bukatar shaidar su a cikin matsala.

Sai Kungiyar ta Kara da yin Kira da a dakatar da dukkan wani aiki da shugaban jami’ar ke cikin dauka tare da kafa wani kwamiti da zai ba ma’aikatan jami’ar kariya da ka iya fadawa cikin matsala bayan bayar da wasu bayanan sirri da kuma batun Karin girman ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: