Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ba da gudummawar Naira biliyan 1 don gina cibiyar jagoranci a jami’ar jihar ta Legas
. Mataimakin shugaban jami’ar ta jihar Legas ne ya sanar da bayar da gudummawar a lokacin taron yaye dalibai na jami’ar karo na 25
. Tinubu ya jagoranci al’amuran jihar Legas daga 1999 zuwa 2007 kuma tun daga nan ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa
Dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya baiwa jami’ar jihar Legas (LASU), gudunmawar kudi don gina wata cibiyar bunkasa ilimin jagoranci da ya kai Naira biliyan 1.
Mataimakin shugaban jami’ar LASU, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello ne ya sanar da bayar da gudummawar a taron lacca yaye dalibai <span;>karo na 25 a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, mataimakin gwamnan jihar Legas Dr. Obafemi Hamzat ne ya wakilci Tinubu a wajen taron.
Da yake magana ta bakin Hamzat, Tinubu ya bukaci gwamnati ta tallafa wa masana’antun dabaru da za su dauki matasa aiki tare da samar da ayyukan yi.
Ya ce tallafin da gwamnati ke bayarwa na kere-kere da masana’antu zai kara bude kofa ga fara sana’o’in da kasuwanci tsakanin matasa.