Home Sashen Hausa Ga ranakun komawa makaranta na wasu jami'o'in Najeriya

Ga ranakun komawa makaranta na wasu jami’o’in Najeriya

Ga ranakun komawa makaranta na wasu jami’o’in Najeriya

University of Lagos

Wasu jami’o’in gwamnati a Najeriya sun fara shirye-shiryen koma wa makaranta daga ranar 18 ga watan Janairun 2021.

Hakan na zuwa ne bayan janye yajin aikin da aka shafe dogon lokaci ana yi a ƙasar, sakamakon daidatawa tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU a ƙarshen watan Disamban da ya gabata.

Majalisar Sanatocin kowace jami’a ne yake da hurumin sanar da ranar komawa bayan janye yajin aikin, kuma ta kan yi hakan ne bayan gudanar da taro don sanya ranar.

Jami’o’i sun shafe tsawon wata tara a kulle sakamakon yajin aiki da kuma dokar kullen annobar cutar korona da ita ma ta kawo cikas a fannoni da yawa, ciki har da na ilimi.

Yajin aikin ya samo asali ne saboda gaza biya wa ASUU buƙatun da ta nema a wajen gwamnatin tarayya tun a shekarar 2019.

Duk da cewa an janye yajin aikin a ranar 23 ga watan Disamban 2020, to dole sai makarantun sun jira matakan da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Yaƙi da Cutar Korona zai ɗauka, a yayin da ƙasar ke fama da hauhawar cutar.

Ga dai wasu daga cikin jami’o’in da tuni suka tsayar da ranar komawarsu.

Jami’ar Bayero Ta Kano (BUK)

A wani taro na musamman da Majalisar Sanatocinn Jami’ar ta gudanar ranar Litinin 4 ga watan Janairu, ta amince da kammala shekarar karatu ta 2019/2020 wadda annobar cutar korona ta yi wa tutsu.

Hakan ya biyo bayan wani gagarumin sauyi ne da aka yi wa tsare-tsaren karatun.

Ga dai yadda abubuwan za su kasance:

Masu karatun digiri na farko za su fara ranar Litinin 18 ga Janairun 2021, sai su kammala zangon karatu na farko ranar Litinin 26 ga Afrilun 2021.

Sai kuma su fara zangon karatu na biyu ranar Litinin 3 ga watan Mayun 2021, sai a rufe zangon ranar 16 ga Satumban 2021.

Sannan hukumar jami’ar ta bayar da tabbacin cewa za ta bi dokoki da matakan hana yaɗuwar cutar korona.

Ga masu karatun digiri na biyu da digirin-digirgir kuwa za su fara zangon farko ne ranar 18 ga Janairu sai su gama shi ranar 5 ga twatan Yunin 2021.

Sai kuma su koma zango na biyu ranar 7 ga Yuni a kammala shi ranar 11 ga Satumban 2021.

Short presentational grey line

Jami’ar Benin (UNIBEN)

Hukumar Jai’ar Benin da ke jihar Edo kuwa ta umarci sabbi da tsofaffin ɗalibai da duk su koma makarantar ranar 30 ga watan Janairun 2021.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da makarantar ta fitar bayan wani zama da Majalisar Sanatocin Jami’ar ta yi ranar Litinin.

Makarantar ta ce zango na farko na shekarar karatun 2019/2020 za ta ci gaba har zuwa ranar 1 ga watan Afrilun 2021, yayin da zango na biyu zai fara ranar 5 ga Afrilun 2021.

Mai magana da yawun makarantar Benedicta Ehanire ya ce, bayan taron Majalisar Sanatocin na 4 ga watan Janairu, sun amice cewa idan ɗalibai suka koma makarata ranar 30 ga wata, to za a fara lakca ranar 1 ga watan Fabrairun 2021.

Sannan hukumar makarantar ta ce za ta bi dukkan dokokin Covid-19, tare da shawartar dukkan ɗaliban da suka san ba su da lafiya da su tabbatar sun warke kafin su koma.

Jami’ar Lagos da LASU

Mai bai wa gwamnan Legas shawara na musamman Tokunbo Wahab ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa dama dukkan makarantun gaba da sakandare na jihar na tsaka da shekarar karatu ne kafin a rufe su.

Ya ce ɗaliban ajin ƙarshe ne za su fara komawa sannan daga bisani sauran su dinga komawa da kaɗan-kaɗan don gudun samun cunkoso a makarantun.

Wannan matakin ya shafi dukkan makarantun gaba da sakandare ne a jihar.

Sai dai ga Jami’ar Lagos da aka fi sani da UniLag wacce ke ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya, hukumomin makarantar sun ce za su gana nan da mako biyu masu zuwa don sanya ranar komawa.

Za mu ci gaba da ƙara bayanai kan wannan labarin da zarar mun samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An yanke wa ‘yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana

An yanke wa 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana ‘Yan Najeriya biyu za su fuskanci da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙasar Ghana...

Darakta Ashiru na goma ya warke daga ciwon da ke damun sa bayan likitoci sun tabbatar da hakan

Fitaccen darakta a masana'antar shirya fina finan Hausa ta KANNYWOOD Ashiru Na goma ya fito daga Abisiti, bayan Likitoci sun tabbatar da cewa yasamu...

Gwamnatin Kano ta Dakatar da muƙaba da Sheikh Abduljabbar

Yanzu-Yanzu: Wata kotun majistari da ke Gidan Murtala a Kano ta dakatar da gudanar da muqabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da sauran malamai, kuma...

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System By Danjuma katsina Since July 2016, the Nigerian Ports Authority (NPA) under the leadership of Hadiza Bala...

Ma’aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya

Ma'aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci ma'aikata a mataki na 12 zuwa ƙasa da...
%d bloggers like this: