Home Sashen Hausa FYADE AKA YI WA MAHAIFIYA TA TA SAME NI- Inji Shugaban kamfanin...

FYADE AKA YI WA MAHAIFIYA TA TA SAME NI- Inji Shugaban kamfanin Black House Media

FYADE AKA YI WA MAHAIFIYA TA TA SAME NI

In ji Shugaban Kamfanin Black House Media

@ Jaridar Taskar Labarai

“Mahaifiya ta ta je aikatau ne, aka yaudare ta, aka yi mata fyade, ta samu ciki na. Wannan ya jefa ta cikin yanayin da ya sa ta yi ta kokarin zubar da cikin, amma ya ki fita. Dole aka haife ni,” in ji Ayeni Adekunle, Shugaban Kamfanin Black House Media, kamfani mafi karfi a yammacin Afrika wajen tallata hajar manyan kamfanoni a kafofin watsa labarai a duniya.

Adekunle, wanda ya fadi haka a hirar da jaridar FORBES AFRICA ta watan Satumban 2019 ta yi da shi, ya bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki a rayuwarsa, amma bai yarda ya kawo masa cikas a nasarar da ya samu a rayuwa ba, wanda har ya mallaki kamfanin da ke da karfin tattalin arziki sama da Dala biliyan 10.

Ya ci gaba da cewa; “Haka Mahaifiya ta ta yi ta gararamba da ni goye a bayanta a birnin Legas, tsakanin aikatau da bara.

“Ina yaro wasu suka sace ni suka kai ni Jihar Kogi, ban sake ganin Uwata ba, sai bayan shekaru 30”, in ji shi.

Adekunle ya kara da cewa; “A can na yi karatun Firamare da Sakandare a wajen wadanda ban san matsayina a wajensu ba, amma sun ba ni kulawa daidai gwargwadon karfin su”.

Ya ce; “Ina gama Sakandare na shiga Jami’ar Ibadan, na rika rayuwa da garin kwaki ba sukari. A nan na hadu da yarinyar da na aura. Daga baya ita ce ta fara canza min rayuwa”.

Ayeni Adekunle ya ci gaba da cewa; “Kudin kashewa ta Naira 500 ne, ita kuma nata Naira 5000 ne. Daga nan ne na fara samun karfin gwiwar yin karatun.

Ya ce a shekarar 2004 ya rasa iyayensa da suke rene shi, kuma a lokacin ya gano Mahaifiyarsa ta gaskiya, bayan shekaru tana neman sa. Mahaifinsa ma ya zo yana rara gefe.

“Ina gama Jami’a na fara rubutun nishadi a jaridu ana biya na, kafin a je ko’ina sunana ya yi tambari. Nan da nan sai manyan ‘yan kasuwar nishadi a waka da barkwanci suka fara dauka ta a matsayin Agent dinsu.

“Sai na fara tafiyar da harkokin Agent na manyan makada da mawaka da masu wasan barkwanci daga gida, daga ni sai matata. Daga nan sai karamin Ofis, sai babban Ofis, sai gina Ofis na dindindin, wanda babu kamarsa a duk yammacin Afrika”.

Adekunle ya ce; “Mun fara yi wa daidaiku aiki ne, amma daga baya sai manyan kamfanoni suka rika kawo mana. Yanzu kusan duk manyan kamfanonin nan da mu suka dogara”.

Ya kalli Dan Jaridar ya ce; “Na yafe wa wanda ya yi sanadin zuwa na duniya ba da aure ba. Na kuma yafe wa Mahaifiya ta da ta yi yunkurin kashe ni kafin in zo duniya”.

A nan ne Dan Jaridar ya ga hawaye na kwarara a kumatunsa suna zubowa daga kwayar idanuwansa.

Yana shasshekar kuka ya ce; “Matasa da yawa na cikin wannan halin, wato an haife su ta hanyar da ba haka suka so ba, in ka ga irin su tausaya masu za ka yi, ka kuma karfafa masu gwiwa, ba kyama ko walakanci ba, don ba su suka kawo kansu ba, kawo su aka yi, kuma ba za su iya jifa ko walakanta wadanda suka kawo su ba. Don haka suna tsaka mai wuya”.

Adekunle ya kara da cewa, su kuma irin wadannan matasan su fuskanci nasarar rayuwarsu su kyale duk wani tunani maras dadi da zai iya takura rayuwarsu.

Black House Media mallakin Ayeni Adekunle da matarsa Ayeni Oladotun, shi ne babban kamfanin da ke yi wa manyan kafofin sadarwa tsarin tallace-tallace, ciki har da MTN da Viacom, Multi Choice.

Ya fara daga gidansa a 2009, ya bude katafaren Ofis dinsa a 2019.

Ya fara da Naira dubu 50, amma yanzu jarin kasuwancinsa ya kai Dala biliyan 10.

Bayan ya yi kudi, wanda ya yi wa Mahaifiyarsa fyade ya zo da niyyar amsar dansa, Ayeni ya ce ba matsala, amma bakin alkalami ya bushe.

Jaridar Taskar Labarai @www.jaridartaskarlabarai.com
Katsina City News www.katsinacitynews.com
The Links News www.thelinksnews.com
O7043777779.08137777245

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here