Fuska biyu muke kallo, fuskar Jihar Katsina da ta jam’iyyar Apc. Inji Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari.

Gwamnan ya fadi hakan ne ranar Alhamis 14/10/2021 a Babban dakin taro na gidan shugaban kasa dake fadar Gwamnatin Jihar Katsina yayin gudanar da taron masu ruwa da tsaki akan zaben shugabannin jam’iyyar Apc na matakin Jiha da za a gudanar ranar Asabar 16/10/2021.

Mai girma Gwamnan ya cigaba da cewa” fatanmu Jihar Katsina ta samu shugaba wanda ya fimu ba wanda muka fi ba, idan aka samu wanda ya fimu shine Jihar Katsina zata kara samun cigaba, domin mu ba gurin mu ace kwanda jiya da yau ba, munaso ace yau tafi jiya.

Da Gwamnan ya tabo batun zabukan shugabannin jam’iyyar na matakin Jiha, wanda ya sanya kiran taron masu ruwa da tsakin, Gwamnan ya jawo hankalin ‘Yayan jam’iyyar musamman shugabannin jam’iyyar da za a zaba da suyi hakuri da abinda aka zartar domin cigaban jam’iyyar Apc, Gwamnan ya kara da cewa” ba kowa ne zai samu abinda yake so ba, amma a sanya albarka da abinda aka samu.

Tunda farko da yake gabatar da jawabin maraba shugaban Kwamitin shirya zabukan shugabannin jam’iyyar na Jihar Katsina Alh. Muntari Lawal ya bayyana irin tsare, tsaren da akayi akan zaben shugabannin jam’iyyar na matakin Jiha da za’a gudanar ranar Asabar 16/10/2021.

Shima a nashi jawabin shugaban jam’iyyar Apc mai barin gado Malam Shitu S. Shitu ya bayyana cewa” ya godema Allah (SWA) akan yadda ya bashi dama ya jagorancin jam’iyyar Apc tsawon shekaru shidda da suka gabata.

Kazalika shugaban jam’iyyar Malam Shitu S. Shitu ya yabama Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari akan yadda yake kokari wajen ganin jam’iyyar Apc ta zauna lafiya ta kuma cigaba a Jihar Katsina. Daga karshe Malam Shitu S. Shitu ya bayyana cewa” zasu bada goyon baya dari bisa dari ga sabon shugabancin jam’iyyar.

Taron ya samu halartar Mai girma Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina QS. Mannir Yakubu, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina Rt. Hon. Tasi’u Musa Maigari Zango, Alh. Dahiru Bara’u Mangal Shugaban tafiyar jam’iyyar Apc a Jihar Katsina, Sanata Abu Ibrahim, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa.

Sauran sun hada da, Sanata Bello Mandiya Sanata mai wakiltar shiyyar Funtua, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, Dr. Dikko Umar Radda, ‘yan majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, ‘yan majalisar zartarwa ta Jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Apc daga ko’ina a fadin Jihar Katsina.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
14 October, 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here