-Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar wa manema labarai harin acid a ranar Talata a Yola, ya ce an kai rahoton harin ga sashen ‘yan sanda na Jimeta a ranar 6 ga watan Janairu, ta hannun Fawas Mohammed, kuma an shigar da karar don bincike.

Akalla mutane hudu da suka hada da wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) an bayyana cewa an kaiwa hari da acid a garin Yola na jihar Adamawa.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa, Sulaiman Nguroje, wanda ya tabbatar wa manema labarai harin acid a ranar Talata a Yola, ya ce an kai rahoton harin ga sashen ‘yan sanda na Jimeta a ranar 6 ga watan Janairu, ta hannun Fawas Mohammed, kuma an shigar da karar don bincike.

“DPO mai kula da sashen ‘yan sanda na Jimeta ya shaidawa rundunar ‘yan sandan jihar cewa wani Fawas Mohammed ya kai rahoton harin acid da aka kai masa tare da wasu mutane uku.

Nguroje ya ce “Bayan sun samu korafin, rundunar ta ba da umarnin gudanar da bincike.”

Sai dai Mohammed, jigo a jam’iyyar APC a jihar, ya yi zargin cewa harin yana da nasaba da siyasa, yayin da yake zantawa da manema labarai.

Mohammed ya yi zargin cewa Abubakar Sarki, jigo a jam’iyyar Yola ta Arewa ne ya shirya hare-haren.

“Bayan sun kai mana hari da acid a karshen Disamba 2021; Haka kuma, a ranar Juma’a, 6 ga Janairu, 2022 da misalin karfe 6:30 na yamma, wasu ‘yan bindiga sun mamaye gidana da ke titin Gimba, Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa.

‘Yan ta’addan sun yi mani wakafi kuma daya daga cikinsu ya gargade ni a fili cewa in daina yin hira a rediyo da sukar gwamnati,” inji shi.

A cewar jigon na jam’iyyar APC, daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya samu munanan raunuka kuma yana karbar magani a asibitin kwararru dake Yola.

A cikin gaggawar mayar da martani, Sarki ya ce hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta gayyace shi kan lamarin. Ya musanta zargin kuma ya bayyana shi a matsayin “Bata masa suna.”

“DSS ce ta gayyace ni a jihar kan lamarin inda na shaida musu cewa ban san komai ba game da harin da ake zargin,” in ji Sarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here