Forbes: Arzikin Dangote da Abdulsamad Isiyaka Rabiu ya ƙaru

Aliko Dangote

Arzikin mutane uku da suka fi kuɗi a Najeriya ya ƙaru cikin shekara ɗaya, kamar yadda mujallarForbes ta bayyana bayan fitar da jerin attajiran duniya na 2021.

Attajiran na Najeriya sun haɗa da shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote da shugaban Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga da kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Isiyaka Rabiu.

Mujallar ta ce arzikinsu ya ƙaru zuwa dala biliyan 22.5 a cikin shekara ɗaya.

Jerin sunayen attajiran duniya da Forbes ta wallafa a ranar Talata ya ƙunshi attajiran Afrika 14 da suka fi kowa kuɗi a nahiyar.

Kuma har yanzu a cewar Forbes, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ne attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka.

Forbes ta ce arzikin Dangote, ya ƙaru inda ya haura $11.5bn daga $ 8.3bn a shekarar 2020, wanda hakan ya sa ya zama mutum na 191 da ya fi kowa kuɗi a duniya.

Shugaban kamfanin Glo da Conoil, Dr Mike Adenuga, wanda shi ne na biyu mafi arziki a Najeriya kuma na biyar a Afirka, shi ne na 440 a duniya inda arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $6.1 daga dala biliyan $5.6 a bara.

Arzikin shugaban kamfanin BUA kuma Abdulsamad Rabiu, arzikinsa ya ƙaru zuwa dala biliyan $4.9 daga dala biliyan $2.9 a bara, kuma shi ne na 574 a jerin attajiran duniya kuma na shida a Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here