Fitaccin mutane da suka mutu a Nigeriya a 2020-BBC hausa

 

Fitattun mutanen da suka rasu a Najeriya a 2020

Fitattun mutanen da suka rasu a Najeriya a 2020

Babu shakka shekarar 2020 ta zo da ba-zata musamman idan aka duba yadda sabuwar cutar korona ta ɓulla a sassan duniya daban-daban inda ta kai har Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana ta a matsayin annobar duniya.

To kuma idan aka yi batun annoba, ba a rasa yin na mutuwa.

A wannan shekarar, Najeriya ta yi rashin mutane da dama– wasu dalilin annobar ta korona wasu kuma dalilin wasu cutukan na daban, ko hatsari.

Za mu yi duba kan wasu daga cikin fitattun mutanen da aka rasa a shekarar ta 2020 da mutane da dama ke cewa ta zo a bai-bai.

Abba Kyari

Marigayi Abba Kyari

Mallam Abba Kyari shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaba Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari tun hawansa mulki a shekarar 2015.

Ya rasu a ranar Juma’a 17 ga watan Afrilu sakamakon cutar korona.

A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa Malam Abba Kyari ya kamu da cutar korona bayan komawarsa Najeriya daga Jamus.

A lokacin da batun rashin lafiyarsa ta bayyana, rahotanni sun nuna cewa Abba Kyari na fama da wata cutar kafin ya kamu da korona.

Jim kaɗan bayan haka, Abba Kyari ya rubuta wata wasika inda ya bayyana cewa ya tafi Legas domin ci gaba da jinya a ƙashin kansa don ya ɗauke wa gwamnati nauyin kula da shi.

Labarin rashin lafiyarsa ya ja hankalin sosai a Najeriya saboda girman muƙaminsa inda a shafukan sada zumunta aka riƙa yayata maudu’in sunansa.

Abba Kyari shi ne babban jami’in gwamnatin kasar na farko da ya harbu da cutar korona.

Ya rasu ne a Legas amma an yi jana’izarsa a makabartar Gudu da ke Abuja a ranar Asabar 18 ga watan Afrilun 2020.

Abba Kyari ya kasance mutum mai ƙarfin faɗa a ji a gwamnatin Shugaba Buhari.

Ɗan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon ɗan jarida ne, kuma tsohon ma’aikacin banki, inda ya riƙe manya-manyan muƙamai a wasu bankunan ƙasar.

Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris

Tsohon Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Alhaji Dokta Shehu Idris ya rasu ne ranar Lahadi 20 ga watan Satumbar wannan shekara.

Sarkin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya a wani asibiti da ke Kaduna yana mai shekaru 84.

Mai martaba Shehu Idris shi ne sarkin Zazzau na goma sha takwas.

An yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Zazzau a garin Zaria inda manyan ƴan siyasa da sarakuna da attajirai na Najeriya suka halarci jana’izar.

Marigayi Shehu Idris ya rasu bayan shafe shekara 45 kan karagar mulki a Masarautar Zazzau.

Tolulope Arotile

Tolulope Arotile

Tolulope Arotile ta kasance mace ta farko a Najeriya da ta iya tuƙa jirgin saman yaƙi.

Ta rasu ne ranar 14 ga watan Yulin wannan shekarar sakamakon hatsarin mota a cikin garin Kaduna.

Rasuwar matashiyar ya jefa ƴan Najeriya cikin alhini saboda kasancewar ta yi suna a wani ɓangare da ba a saba ganin mata a cikinsa ba a ƙasar.

Haka kuma ta rasu ne tana da shekaru 22 a duniya.

Tolulope Arotile ƴar asalin Ƙaramar Hukumar Ijumu ce da ke Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya amma ta girma ne a Kaduna.

Ta fara karatun firamarenta a makarantar sojojin sama ta Nigeria Airforce Primary sannan ta halarci sakandaren Airforce.

Hakan ya ba ta damar share wa kanta hanyar shiga aikin soja tun tana ‘yar ƙaramarta.

Babu jimawa ta gama samun horo na musamman a cibiyar Starlite International Training Academy a Afirka Ta Kudu, kuma ta samu kyakkyawan sakamako.

Kazalika ita ce ɗaliba mafi hazaƙa lokacin da ta kammala karatu a rundunar Sojan Sama ta Najeriya a shekarar 2017.

Bayan rasuwarta ne bayanai suka fito daga rundunar sojin ƙasar kan yadda Tolulope ta rasu inda aka bayyana cewa wani tsohon abokin karatunta ne ya bankaɗe ta da mota ba tare da saninsa ba.

Sama’ila Isa Funtua

Sama'ila Isa Funtua

Kafin rasuwarsa, Malam Sama’ila Isa Funtua ya kasance ɗaya daga cikin manyan makusantan Shugaba Muhammadu Buhari.

An haifi Sama’ila Isa a shekarar 1942 a jihar Katsina kuma sun ƙulla abota da shugaban ƙasar tun suna ‘yan yara.

Malam Sama’ila ya rasu ne ranar 20 ga watan Yulin shekarar 2020 sakamakon bugun zuciya, bayan ya faɗa wa iyalinsa ba ya jin daɗi.

“Mallam ya faɗawa iyalinsa cewa yana son ganin likita amma sai da ya fara zuwa wajen mai aski. Daga nan kuma ya tuƙa mota zuwa asibiti,” in ji ɗan uwansa wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa.

Isma’ila Isa Funtua ɗan kasuwa ne kuma jami’in gwamnati da ke da ƙwarewa sama da shekara 30.

Marigayin ya taɓa riƙe muƙamin minista sannan ya taɓa jagorantar ƙungiyar masu buga jarida ta NPAN na tsawon shekara takwas.

Shi ne ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin ƙere-ƙere da ya gina muhimman wurare a Abuja, babban birnin Najeriya.

Alhaji Isma’ila Funtua ne daraktan gudanarwa na farko na jaridar Democrat.

Haka kuma, ɗan Malam Sama’ila Funtua Abubakar na auren ƴar Shugaba Muhammadu Buhari, Safina.

Janar Domkat Bali

Domkat Bali

Janar Domkat Bali ya rasu ne ranar 4 ga watan Disambar wannan shekarar yana da shekaru 80 a duniya.

Janar Bali ya taɓa riƙe muƙamin ministan tsaro kuma mamaba na majalisar ƙolin soja tsakanin shekarun 1984 zuwa 1990.

A lokacin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na Mulkin Soja, Janar Bali ne shugaban ma’aikatansa tsakanin shekarar 1984 zuwa 1985.

Rahotanni sun bayyana cewa janar ɗin ya mutu ne a birnin Jos na Jihar Filato bayan fama da rashin lafiya, yayin da a ke shirin kai shi ƙasar waje domin neman magani.

Ya rasu ya bar matar aure ɗaya da ƴaƴa biyu.

Malaman jami’a da kwaleji da malaman Islama na Kano

kano deaths

A cikin watan Afrilu ne aka rasa mutane da dama a jihar Kano ciki har da manyan malama jami’a da kwaleji da malaman addinin Musulunci .

Mace-macen sun zo ne a dai-dai lokacin da annobar korona ta ke kan ganiyarta a faɗin duniya ciki har da Najeriya.

Sai dai ba a tabbatar ko cutar ce ta janyo yawan mace-macen ba a jihar ta Kano. Daga cikinsu akwai Farfesa Ibrahim Ayagi da Farfesa Aliyu Umar Dikko da Farfesa Balarabe Maikaba da Ustaz Dahiru Rabi’u da Malama Halima Shitu.

Sannan akwai Sheikh Tijjani Tukur Yola da Dr Sabo Kurawa da Dr Uba Adamu da Dr Ghali Kabeer Umar da Malam Abdullahi Lawan da Malam Musa Ahmad Tijjani.

Tsohon shugaban NNPC Maikanti Baru

Maikanti Baru

A ranar 30 ga watan Mayu tsohon Shugaban Kamfanin Mai na Kasa a Najeriya, NNPC Maikanti Baru ya rasu.

An haifi marigayin a garin Misau na jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya a 1959 kuma ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria 1982 inda ya yi karatu a fannin Injiniya.

Ya soma aiki a babban kamfanin man na Najeriya a 1991 inda ya yi ta samu karin girma har ya kai ga zama shugaban na NNPC.

Maikanti Kacalla Baru ya rike mukamin shugaban NNPC daga 2016 zuwa 2019 bayan ya yi aiki a sassa daban-daban na bangaren mai a Najeriya.

Fitaccen mai kama barayi, Ali Ƙwara

Ali Kwara

Ali Ƙwara

Ali Kwara

A ranar Juma’a 6 ga watan Nuwamba ne Allah Ya yi wa fitaccen mafaraucin nan kuma mai kama barayi, Alhaji Ali Kwara inda aka yi jana’izarsa a mahaifarsa ta Azare a ranar Asabar.

Ali Kwara ya rasu ne a wani asibiti a Abuja bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sam Nda-Isaiah: Mawallafin jaridar Leadership

Sam

A ranar 11 ga watan Disamba ne mawallafin jaridun Leadership da ake bugawa a Najeriya Mista Sam Nda-Isaiah ya mutu.

Iyalan marigayin sun sanar da BBC cewa ya rasu ne bayan wata gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Mista Sam ya mutu yana da shekara 58.

A wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya Femi Adeshina ya fitar, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma na hannun damansa na siyasa.

Ƙarin labaran da za ku so

NO COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

%d bloggers like this: