TB Joshua: Fitaccen mai wa’azin Kiristocin nan dan Najeriya ya rasu

Fitaccen mai wa’azin Kiristocin dan Najeriya TB Joshua ya mutu.

Ya rasu ne ranar Asabar da daddare a birnin Lagos yana da shekaru 57 a duniya.

Wata sanarwa da cocinsa mai suna The Synagogue Church Of All Nations (SCOAN) ta fitar da safiyar Lahadi ta tabbatar da mutuwar Fasto Joshua.

Sanarwar da cocin ta fitar ta ce: “Ubangiji ya dauki rayuwar bawansa Prophet TB Joshua zuwa gida – bisa ikonsa kamar yadda ya kamata. Ya mutu ne yana bautar Ubangiji. Wannan shi ne abin da aka halicce shi domin ya yi, kuma shi ya rayu yana yi, kuma ya mutu yana yi.”

Sanarwar ta ambato wata aya ta liffafin Injila wadda ke cewa: “Tabbas Allah mai girma ba ya yi komai ba tare da bayyana shirinsa ga bayinsa annabawa ba.” – Amos 3:7

Ranar Asabar 5 ga watan Yunin 2021, Prophet TB Joshua ya yi jawabi a wajen taron hadin gwiwa na Emmanuel TV Partners Meeting: “Komai yana da lokaci – lokacin da ya kamata mu zo nan mu yi addu’a da kuma lokacin da ya mu koma gida bayan bauta.”

Prophet TB Joshua yana cikin masu wa’azin da ke jawo ce-ce-ku-ce inda shahara wajen yin hasashen abubuwan da za su nan gaba lamarin da wasu ke ganin karambani ne da katsalandan kan ayyukan Ubangiji.

A shekarar 2014, mai wa’azi ya sha suka bayan rufin cocinsa da ke Najeriya ya rufta kan masu ibada lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 116.

Tarihin TB Joshua

An haifi Temitope Balogun Joshua da aka fi sani da TB Joshua ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1963 a garin Arigidi na karamar hukumar Akoko North-West da ke jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya.

Prophet TB Joshua fitaccen mai wa’azin Kiritoci ne da ke yin bushara a talabijin.

Shi ne ya kafa cocin The Synagogue, Church of All Nations (SCOAN) wadda ke yin wa’azi kai tsaye a kafar talbijin ta Emmanuel TV da ke birnin Lagos.

Prophet TB Joshua yana da coci-coci a kasashe da dama kuma ya shahara a Afirka da Latin Amurka.

Rahoton BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here