Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
05/05/23
A farkon shekarar 1998, aka fara wallafa jaridar Weekly Trust a Kaduna. Jaridar tana fitowa mako-mako, a duk ranakun Juma’a.
Ƴan Arewa da dama sun yi maraba da samuwar wannan jaridar a lokacin saboda ta maye mana manyan guraban da New Nigerian da mujallar Citizen (da tsaffin jagororin New Nigerian irinsu Muhammed Haruna da Bilkisu Yusuf da Adamu Adamu da kuma Kabiru Yusuf mawallafin Weekly Trust ɗin suka kafa) suka bari.
Abokina Yunus Ahmed shaida ne, yadda a lokacin muka ɗaura wa kanmu adashin sayen jaridar Weekly Trust ko wane mako. Wani makon in saya ya saya. Wani makon ya saya in karanta.
A wancan lokacin cikin zaƙaƙuran marubuta a jaridar akwai Sanusi Lamido Sanusi da Aliyu Usman Tilde. Har yanzu za’a iya samun ire-iren rubuce-rubucen da Sanusi yayi a Weekly Trust a taskance a dandalin gamji.com. Rubuce-rubucen Aliyu Tilden ne kawai bana da tabbacin inda za’a same su a taskance.
Su waɗannan mutanen guda biyu su suka fara kawo cecekuce akan fifikon Fulani da Fillanci akan Hausawa da sauran ƙabilu a rubuce-rubucen su na wannan lokacin. Suke nuna cewa Fillani kaɗai ke da daraja da baiwa da basira da sanin makaman mulki, har suna cewa wai saboda Janar Buhari bafillacene shiyasa yafi Janar Babangida wanda ba bafillaceba sanin makaman mulki da iya mulki. Yanzu dai duk ƴan Nijeriya sunga irin kamun ludayin Buhari wajen iya mulki.
Bana mancewa akwai ɗayansu da ke cewa wai ya kamata in sarautar Sokoto ko Kano ko Katsina ko Zazzau ta faɗi, duk wanda zai nemi wannan sarautar sai an gwada shi anji in yana jin Fillanci! Watau duk ɗan Sarkin da baya jin Fillanci, jinin Danfodiyo ko Dabo kawai bai wadatar ya zama Sarkin Musulmi ko Sarkin Kano ba. A taƙaice basu gamsu da fillancin bafillacen da baya jin fillanci ba. (Me ma ya kawo maganar jin fillanci a sarautar da aka ce an kafa da sunan addini?).
Akwai wani mazaunin Ƙofar Sidin Abakwar Kaduna da ya maida masu martani aka buga a jaridar a Weekly Trust a lokacin. A ciki yake masu shaguɓen yadda daraja da fifikon Fillani a kan sauran ƙabilu ta bayyana wajen ƴaƴan Fillani masu tallar nono wajajen Bega ta Abuja da ake gani da idanu shuɗaye irin na Turawan Jamus!
Wannan martani na mazaunin Kofar Sidi, ya burgeni matuƙa a lokacin har na yanke shafin jaridar na adana cikin kaya. Sai dai a yanzu saboda shekaru da yawan iyali zai yi wuya in iya tuna inda wannan takardar take.
Wannan mutumin mai ganin fifikon Fillani a kan sauran ƙabilu shine ƙaddara ta kai zuwa bisa ƙaragar sarautar Kano. Shine a gabagaba wajen yaɗa bidi’ar cewa ‘xth Fulani Emir of Kano’.
Bana mancewa, nasan wasu cikin masu karatun wannan rubutun nawa zasu iya tunawa, yadda a farkon zamansa Sarkin Kano aka rinƙa yaɗawa a kafafen soshiyal midiya, wai zai yi jawabi da Fillanci a fadar Kano! Ina kyautata zaton wasu masu hangen nesa ne suka taka wa abun birki. Shiyasa muka ji shiru.
Saƙon da nake ƙoƙarin isarwa anan shine, in har ana neman waɗanda suka fara assasa wutar ƙabilanci tsakanin Fillani da Hausawa/sauran ƙabilu, kada a mance da gudummawar da Sanusi da Tokorana Aliyu Tilde suka bada.
Da kamfanin Trust zai bani damar duba ma’ajiyar jaridun Weekly Trust na shekarun farko, na san zan fiddo waɗannan rubuce-rubucen kowa ya gansu insha Allahu.
Wannan mutumin mai tinƙaho da fifikon Fillani a kan sauran ƙabilu shine bayan an tsige shi daga sarautar Kano, ya shiga ya fita har sai da aka naɗa shi jagoran Fillanin duniya. Kuma wai shine wasu ke wa fatan ya sake komawa bisa karagar sarautar Kano, Jalla Babbar Hausa ko Jallabar Hausa a matsayinsa na shugaban kungiyar Fillani ta duniya!
Ayi dai mu gani in tusa zata hure wuta!
Hausawa sunce waiwaye adon tafiya, duk tafiyar da ba’a waiwaye tana cike da tasgaro, saboda ba za’a fahimci inda aka fito ba, balle a gane inda aka dosa.
Aliyu Ammani
U/Shanu Kaduna
05/05/23