A yau asabar 21-01-2023 makarantar Madarastul Madinatul Ahbab Wattalamiz Littahfizul ƙur’an ƙarƙashin jagorancin Shehu Ɗan-Almajiri ta Alhaji Shehu Na-Bilki Batsari Khadimul Ƙur’an, tayi bikun yaye ɗalibai karo na shidda a harabar makarantar dake bakin asibiti Batsari a jihar Katsina, Najeriya.
A wannan karon makarantar ta yaye ɗalibai 37 da suka sauke alƙur’ani mai girma, sanna an yaye ɗalibai biyar (5) da suka haddace alƙur’anin, ga jerin sunayen ɗaliban da suka haddace alƙur’ani;
1.Fahad Ibrahim
2.Muhammad Musa
3.Aisha Abdullahi
4.Jamila Usman
5.Fatima Sa’adu.
A jawabin da ya gabatar a wajen taron shugaban ƙaramar hukumar Batsari Alhaji Yusuf Mammam Ifo (Yanji) yayi kira ga al’ummar ƙaramar hukumar Batsari da su duƙufa wajen bada mahimmaci ga karatun alƙur’ani domin a faɗar sa matsalolin da yankin yake ciki bai rasa nasaba da yin saku-saku da karatun alƙur’ani. Daga ƙarshen jawabinsa ya shelanta bada gudummuwar naira dubu ɗari ga asusun wannan makaranta.
Shima a nasa jawabin sarkin Ruman Katsina hakimin Batsari Alhaji Tukur Muazu Ruma yayi kira ga al’ummar yankin da suji tsoron Allah su ilimtar da ƴaƴansu karatun ƙur’ani da na zamani domin zaayi masu tambaya game da yadda suka rayu da ƴaƴan da suka haifa a gobe ƙiyama.
Sauran manyan baƙi da suka halarci taron, watau; Dr. Abdulrahman Kabiru Salga Kano, Halifan Shehu Saadu hayin gada Dutsinma, Sheikh Tijjani halifan halifan shehu Ɗan-almajiri, da sauransu, sun miƙa godiyar su da jinjinar ban girma ga wanda ya assasa wannan makaranta watau Alhaji Shehu Na-Bilki, inda sukayi fatan Allah ya saka masa da mafificin alheri. A cikin jawabinsa Dr. Salga ya zayyano falalolin ƙur’ani mai tsarki a duniya da ma lahira ta yadda zai ceci maabocin karanta shi a gobe ƙiyama.
