Man Utd na fatan kara daukar yan wasa a kalla guda hudu kafin a rufe kasuwa. [@JBurtTelegraph]
Abdou Diallo ya yanke shawarar kin amincewa da komawa AC Milan saboda bai gamsu da yanayin tsarin da aka gabatar masa ba na wasanni. [@Tanziloic]
Juventus ta cimma yarjejeniya da PSG kan Leandro Paredes a matsayin aro tare da zabin saye a kan Yuro miliyan 15. [L’EQUIPE]
.
Dan wasan baya na Borussia Dortmund Manuel Akanji shi ne lamba 1 da Leicester ke nema idan an sayar da Wesley Fofana. [Telegraph Football]
Chelsea na shirin wani sabon tayi na kusan fam miliyan 75 kan Wesley Fofana – har yanzu tana yanke shawarar tsarin tayin tare da kari. Leicester, tana jiran karbar sabon tayin yanke shawarar. [Fabrizio Romano]
Lyon taki amincewa da tayin da West Ham United ta yi na dan wasan tsakiya Lucas Paquetá. Yanzu OL na neman sama da €60m. West Ham ta yanke shawarar ko za ta koma cinikin ko kuma ta mai da hankali kan wani dan wasan. [@skysports_sheth]
.
Everton ba ta son siyar da Anthony Gordon duk da cewa Chelsea na son biyan fan miliyan 60 kan dan wasan mai shekara 21. [Sky Sports]
.
Sha’awar Newcastle kan Joao Pedro ya ƙare a wannan kasuwar musayar ‘yan wasa. Magpies ba su amince da farashi ko yarjejeniya da Watford ba. [@LukeEdwardsTele]