Najeriya,kasa mai yawan kabilu,yare da addinnai,ta yi fama da rikice-rikice masu nasaba da kabilanci,bangaranci da addini. Abin da ba za a manta da shi ba,shi ne rikicin zaben 12 ga watan Yuni ( June 12). An sha fama,kafin a sake dinke wannan baraka da ta kusan sanadiyyar ruguza kasar nan.
Daga karshe,mulki ya koma kudu,inda Obasanjo yai shekara takwas da ya gama,mulki ya sake dawowa arewa. Yanzu dan Arewa,zai gama shekara takwas.Tambaya a nan ,ina yakamata mulki ya koma?
Ya ,’Yan Najeriya ,ai koda ido ba mudu bane ,amma ai yasan kima. Idan za ai adalci,a kuma cire son zuciya,to yakamata mulki ya koma kudu.
Wannan yasa babu Wanda yakamata al’ummar Arewa su zaba,a zaben shekaran nan ta 2023 ,da ya wuce dantakarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC,ASIWAJU BOLA AHMED TINUBU,JAGABAN BORGU.
Wannan sako ne daga:
GAMAYYAR KUNGIYOYIN KATSINA MASU RAJIN HADIN KAI DA DINKEWAR NAJERIYA.