Ya lashe zaben ne bayan wata zazzafar fafatawa
Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya lashe zaben fid-da gwani tare da zama dan takarar Gwamna na jam’iyyar PDP na Jihar Kogi.
Hakan sai na nufin shi ne zai tsaya wa jam’iyyar takarar Gwamna a zaben na ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Sanata Dino Melaye ya sami nasarar lashe zaben ne bayan ya doke abokan takararsa a zaben da fafatawa ta yi zafi a cikinsa.
Tsohon dan Majalisar Dattijan dai zai fafata ne da Usman Ododo, dan takarar kujerar na jam’iyyar APC a zaben da ke tafe.
Source:
Daily Trust
Via:
Katsina City News