Daga JESUTEGA ONOKPASA
Ban taba karanta wata makalar da take cike da tantagaryar karya da shaci-fadi fiye da makalar Dakta Sani Sabo mai taken “Shirin Tinubu na murkushe Arewa” ba.
Wannan bahaguwar makalar, mai tunzura jama’a da jaridar Daily Trust ta buga a ranar 4 ga Nuwamba, ta yi ikirarin cewa kundin manufofin kamfen din takarar Shugaban kasa na Tinubu da Sanata Kashim Shettima na da nufin “kara jefa” Arewa cikin “kangi na rugujewa,” ko ma me hakan ke nufi.
Duk da cewa yawancin abin da Sabo ya kattaba yana bayyanar da tsantsar jahilcinsa da rashin kan gado, kuma cike yake da bayanan da suke a sarari karairayi ne da soki-burutsu da sam ba su cancanci ma a tanka musu ba, amma akwai wasu karairayin da yake tutiya da su da ya kamata a musa masa su.
Da farko dai, ta yiwu Sabo yana fede wani kundi ne, ba wannan kundin da aka yi wa take “Kundin manufofin sabuwar fatan Tinubu/Shettima” ba, don kuwa ya yi ikirarin cewa kundin “wai yana son mai da Arewa wani yankin da yaki ya tagayyara, da kullum ke jiran taimako.
Ko ba a fada ba, wannan karya ce tsagwaron ta.
A madadin haka, Kundin tsare-tsaren Tinubu-Shettima yana da nufin cusa wani sabon fata ne a yankin da a yau yake fama da matsaloli na ta’addanci da hare-haren ’yan bindigan daji.
Dangane kuwa da abin da Sabo ya kira “Mai da Arewa saniyar ware a tattalin arziki,” wannan shi ne bayani na rashin gaskiya dangane da halin da Arewacin kasarmu take ciki, musamman ma da yake ya fito ne daga bakin wani wanda da gani wani sojan baka ne na siyasa da yake riya cewa yana magana ne a madadin Arewa. Da fari ma dai tukun, da wuya mutum ya iya kafa hujjar cewa matsalolin tattalin arzikin da Arewa ke fama da su sun samo asali ne daga mai da ita ‘Saniyar ware’, alhali ita Arewar nan ta fi kowane yanki samar da shugabanni a kasarmu. Ko ma da mene ne, Sabo ba shi da cikakkiyar masaniya dangane da tattalin arzikin da ya so ya labe da shi wajen sukar tsararren kundin kamfen din da bai ma fahimci inda ya sa gaba ba.
Duk da cewa da gaske ne Arewa na fama da matsalolin zamantakewa da na tattalin arziki da ya kamata ya dami duk wani dan kasar nan, amma a lokaci guda ba za a ce ai Kudancin kasar nan kuma wani yanki ne da yake ci gababbe ta fuskacin tattalin arziki, inda ake sharbar romon dimokradiyya yadda ya dace ba. Bisa ga dukkan alamu, shi kansa Sabo na bukatar a karantar da shi ilimin tattalin arziki na hakika, sabanin ra’ayinsa irin na teburin mai shayi da ya dora makalarsa a kai. A hakikanin gaskiya, babban tarnakin da ke damun ci gaban Arewa ta fuskacin tattalin arziki shi ne rashin mai da hankali wajen gina mutanen yankin da kuma dakile mata cikin shiga harkokin bunkasa arziki a yawancin sassan yankin.
Idan a wani sashe, kashi 80 cikin 100 na jama’arsa ana damawa da su a fagen ilimi da tattalin arziki, wanda ba ruwansa da jinsin mutum, to ai kuwa dole zai zamo a wannan fannin, yana gaban wani yankin da mafi yawancin jama’arsa ba su da ilimi kuma an katange mata daga shiga harkokokin bunkasa tattalin arziki. Wannan wata gaskiya ce mai daci da shi ne ginshikin bambancin da ake gani ta fuskacin tattalin arziki tsakanin Arewa da kudu, wanda ya kamata ya dami dukkan shugabannin Arewa da Kudun, kuma ya kamata su yi i’itirafi da haka nan. Wannan shi ya kamata a fuskanta maimakon kirkirar karairayi da dora laifi a inda bai dace ba da shugabannin boge irin su Sabo suke yi, wadanda yadda suke fuskantar matsalolin Arewa ba zai haifar da da mai ido ba, maimakon haka ma zai kara dagula lamurran da tuni suka kazance ne.
Soke-soken da Sabo ya yi wa Shugaba Buhari ba su da madafa, kuma a sarari hakan ya samo asali ne daga jahilcinsa kan tattalin arziki da kuma mummunar aniyar da yake da ita ta haifar da rudani. Ai a duk tarihin Nijeriya, babu wani Shugaban kasa na mulkin farar hula ko soja da ya yi kokarin ci gabantar da Arewa fiye da Muhammadu Buhari. In ma akwai wani Shugaban kasa da ya yi iya kokarinsa, to zai zama Shugaba Goodluck Jonathan ne, amma ba wani shugaba da ya fito daga Arewar ba.
Ya kamata a lura fa, duk da karancin kudin da ake samu daga cinikin man fetur, gwamnatin Buhari ta iya tabuka rawar da ana iya cewa wata mu’ujiza ce, a fannin samar da isasshen abinci ga kasa da ma sayar da saura zuwa kasashen duniya. Wannan fa duk a bayan horarwa kan sana’o’in hannu, da ba da tallafi ga matasa da kanana da matsakaitan kamfanoni. Magana ta gaskiya, ba wata gwamnati da ta yi kyakkyawan tasiri a duk fadin kasar nan, musamman ma dai a Arewa, fiye da gwamnatin Buhari. Sai dai kawai a ce gwamnatin ta fuskanci dagulewar al’amura daga matsalolin ’yan ta’adda a Arewa da kuma barayin man fetur a Kudu.
In dai batun ta’addanci ne, Sabo, duk da ya yi kokarin riya cewa ya damu da halin da wadanda abin ya shafa suke ciki, sai da ya rika sukar gwamnatin Buhari da ta rika dadadawa wadanda suke gudun hijira da kuma al’ummun da ta’addanci ya tagayyara. Wai shin ma wace irin akidar tafi da mulki Sabo yake bi ne? Shin ra’ayin Gwamnatin da take nuna halin jimina kan abin da ya shafi ‘yan gudun hijira kamar yadda Sabo yake yi ga matsalolin Arewa na hakika yake bi?
Wannan tashin hankalin da ake fama da shi a Arewa, tsattsauran ra’ayin addini ne ke hura shi, wanda a duk duniya ma ya zama gagarabadau, kuma da wuya a iya kau da shi gaba dayansa. Ni ra’ayina kan tsattsauran ra’ayin addini shi ne ’ya’yanmu da ke tafe za su fi karfinsa, har ma a wayi gari an turbude shi a jujin tarihi. A yayin da Sabo ke zargin gwamnati da ba da taimako ga wadanda ta’addancin ya shafa maimakon kau da ta’addanci, ya kuwa san cewa yana tozarta kansa ne a matsayinsa na mai rike da digirin digirgir? Shin Amerikawa duk da irin karfinsu, ba guduwa suka yi suka bar ladansu, suka yarda cewa sun sha kaye yayin fada da ta’addanci na shekaru 20 a Afghanistan? Me Sabo yake nufi da ya ce wai “an bar rashin tsaro na cin karensa ba babbaka,” kamar yadda ya ce?
Me Sabo yake son cewa ne? Ya dora laifin tsattsauran ra’ayin addini a Arewa kan Buhari? Shi kansa Buhari ba ’yan ta’adda sun kusa kashe shi ba lokacin da suka kawo masa hari sa’ilin da yake neman zama shugaban kasa? Wannan fa wata matsala ce ta kasa da kasa wacce take neman gagarar kasashen duniya! Wai me ya sa wasun mu suke son kantara karya ko kunya ba sa ji duk saboda siyasa? Kowace gwamnati in dai tana fuskantar ta’addanci, to dole ne ta rika ba da tallafi da taimako ga wadanda abin ya shafa, a lokaci guda kuma tana iya kokarinta wajen dakile bunkasar ’yan ta’addan, in ba haka ba kuwa, to sai a ce ta gaza. Shin Sabo wanda yake ikirarin yana da digiri har uku zai ce bai san da hakan ba?
A tsawon makalarsa, Sabo ya rika fadawa kan abin da kawai za a iya bayyana shi ne da kuka irin na jahilci. A cewarsa fa, “ta yaya za a ce wasikar neman wata bukata sai ta samu amincewar wani Shiugaban bankin kasuwanci a Lagos kafin na soma harkokin kasuwanci na a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina, misali? Ya za a ce hakan ya dace?” Wannan wane irin shirme ne? Wannan ma shi ne sashen da ya fi fito da kidahumancin Sabo a dukkan makalar tasa. Idan fa aka biyewa rashin kan gado irin na Sabo, mutumin da ke Gashua a Yobe ko Zuru a Kebbi zai iya tunanin me ya sa wani aikin ci gaba na gwamnatin Tarayya wanda zai amfane su za a ce sai ya samu sa hannun amincewa daga Abuja, haka ma mutumin da ke Sapele a Delta ko Obudu a Kuros Ribas zai iya yin irin wannan tunani!
Ba Tinubu ko gwamnatin Tarayya ne suka sa Lagos ta zama hedikwatar yawancin bankuna ba. Su fa bankuna, kamar sauran kamfanoni, ciki har da babban kamfanin nan na Aliko Dangote, suna kafa hedikwatarsu ne inda suka ga ya fi dacewa ta fuskacin tattalin arziki. To, ai ma shi ya sa muke kasa daya, mai tattalin arziki iri daya. Me ya sa Ba’amurke da ke birnin Seattle, da Washington ba zai buga kansa ga bango ba saboda sai ya sami sa hannun amincewa daga bankin da ke da hedikwata a Wall Street, New York ko wata hukuma da ke Washington DC, wadanda duk biyun nan nisan da ke tsakanin su da birnin Seattle kamar nisan da ke tsakanin Dakar da ke Senegal ne da Kanon Nijeriya?
Dangane hukuncin da Sabo ya zartar cewa, kundin kamfen na Tinubu/Shettima “na yi wa Arewa kallon wani fagen yaki da nufin ta’azzara lamarin,” ta yaya mutumin da ke riya cewa shi mai sharhi ne kan al’amuran yau da kullum zai iya samun darfin halin yada wannan karya mara tushe? Ba wanda ke wa Arewa kallon wani fagen yaki – ai Arewa wani fagen yaki ne a wasu yankunan, kuma abin da zai kara dagula wannan mummunan lamari mai ban takaici shi ne kawai tsukakken tunani na mutane irin su Sabo, wadanda suka kasance masu tsattsauran ra’ayin kabilanci da bangaranci, wadanda tun asali sune matsalar Arewa, kuma a haka suke so su kasance.
Abin da mutane irin su Sabo ba su gane ba shi ne, mutanen kirki na Arewa tuni suka dawo daga rakiyarsu da karairayinsu da ra’ayinsu na bangaranci. Akwai wani ittifaki na siyasa da aka yi a kasar nan cewa, mulki ya kamata ya zakuda zuwa Kudu a 2023, kuma wannan wani ra’ayi ne da ke da tagomashin su kansu ’yan Arewa bisa jagorancin Gwamnoni da sauran shugabannin yankin. Duk yadda irin su Sabo suka so yi a rubuce don saboda Atiku Abubakar na PDP, su rubuta kage da tunzura jama’a, to ba zai yi nasara ba a shirinsa na shigewar fadar Aso Rock ta yanke. Ko ma dai yaya ne, in Atiku ya zama shugaban kasa, to Kudu da ke tsananin adawa kuma take ganin an cuce ta wajen samar da Shugaban kasa na gaba, za ta fada cikin rashin kwanciyar hankali ne kamar yadda Arewa take fama da shi a halin yanzu, don haka ire-iren su Sabo tun yanzu sai su soma tunanin ina kasar da wanda suke wa kidin zai samu ya mulka?
Duk da cewa Sabo zai iya rudar kansa ya dora alhakin matsalolin Arewa kan Bola Tinubu da Kashim Shettima, gaskiyar ita ce, in har Tinubu ko Shettima za a iya zargin sa kan wani abu, to sai dai a zarge su da samar da sabbin dabarun tafi da mulki kamar yadda duniya shaida cewa cewa sun yi abin da ya dace a Lagos da Borno bi da bi.
Irin wannan kyakkyawan manufa da kwarewar mulki ce fa Bola Tinubu ya aiwatar a lokacin da yake Gwamnan Lagos, kuma Kashim Shettima ya bi a Borno, kuma ake bukatar a bi a duk fadin kasar nan, musamman a Arewar da ire-iren su Sabo suka haifar da mummunan halin da take ciki.
Alal hakika irin ra’ayoyin da Sabo yake so jama’a su fahimta, ra’ayoyi ne na son rai da suka hana Arewa musamman, ci gaba ta fannoni da dama, da ma kasar gaba daya. Sabo da ire-irensa za su kyauta wa kansu ne in sun rufe bakunansu, tare da barin fagen ga ‘yan gaba dai-gaba dai irin su Shettima a Arewa, wadanda suna da abin nunawa na alheri da suka yi ga yankin Arewar da ma kasar baki dayanta.
A Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, muna shirin samun Shugaban kasa wanda a duk tsawon ayyukansa na mulki ya nuna yana da kwarewar da yakan bar wuri fiye da yadda ya same shi. A takaice dai Tinubu dan birni ne wanda yake mai da kauye gari, ya mai da gari birni, ya mai da birni babban birni. Shi kuwa Kashim Shettima, daf muke da samun Mataimakin Shugaban kasa wanda ya ki rusunawa ga ta’addanci, wanda ba zai rude ba idan yaki ya fuskanto shi gadan-gadan, wanda kuma ya iya tafiyar da mulki duk da irin harsasan da suka rika gitto masa da mutanensa.
Ba kamar yadda Sabo ya yi kokarin nunawa ba, cewa ana so a murkushe Arewa, to tambarin kamfen na Tinubu wani zane ne da ke nuna cewa an karya duk wani kaca da ke wa Arewar tarnaki. Idan dai har Sabo da masu ra’ayi irin nasa da gaske sun damu da Arewa, to ina mai farin cikin sanar da su cewa, taimako na nan tafe a kan hanya, kuma maganin da ya dace da Arewa kuma take tsananin bukatar sa a wannan lokaci, wanda ma za a iya samun sa a kowane shagon sai da magunguna shi ne “Sai Tinubu da Shettima”.
Onokpasa, lauya, kuma memba na kwamitin kamfen na jam’iyyar APC, ya rubuto ne daga Abuja.