Home Sashen Hausa FATIMA BUHARI TA TAIMAKAWA MARASA LAFIYA A DAURA

FATIMA BUHARI TA TAIMAKAWA MARASA LAFIYA A DAURA

FATIMA BUHARI TA TAIMAKAWA MARASA LAFIYA A DAURA

Daga Suleman Harris daura

A ranar litinin 7th December, 2020 kungiyar Khamms Charity Foundation tare da hadin gwiwar kungiyar kwararrun likitocin mazauna Nigeria (NARD), karkashin shugabancin diyar Shugaban kasa Hajiya Fatima Muhammadu Buhari, ta gabatar da shirin tallafawa marassa lafiya masu fama da ciwon sikari, hawan jini, zazzabin cizon sauro da sauransu, ta hanyar basu magani, tare da tallafin kayan abinci.
A cikin jawabinta Hajiya Fatima Muhammadu Buhari ta yabawa mahalarta taron da wadanda suke taimakawa kungiyarta cikin shirshiryenta da bada shawarwari don samun nasara. Sannan ta nuna kudirinta na ganin ta taimakawa mabuta ba tare da yin la’akari da duk wani banbanci na yanki, addini, kabilanci da sauransu.
Daga bisani ta kewaya cikin asibitin cikin dakunan kula da marassa lafiya domin ta duba marassa lafiya.
A wani bangaren Kuma Dr. Uyi Shugaban kungiyar kwararrun likitoci mazauna Najeriya ya bayyana kudirinsa na tabbatar da bada kulawarsu ta musamman ga masu rashin lafiyar magani.
Manyan baki da suka halarci taron sun hada da wakilin mai martaba sarkin Katsina Alh. Sani Madawaki (Deputy Accountant General katsina state), wakilin mai martaba sarkin Daura Alh. Auwalu Umar Farouq Sardaunan Daura, Member National assembly Hon. Fatuhu Muhammad, Shugaban Mulki na Karamar hukumar Daura Alh. Hussaini Umar Rafin dadi, Alh. Musa Umar Magajin garin Daura, Wazirin Dan Madamin Daura Hamisu Haro, Hajiya Ambarud Sani Wali da sauransu.
Masu gabatar da bayanai a cikin taron sun bayyana farin cikinsu da yabawa Hajiya Fatima Muhammadu Buhari wurin kyakykyawar niyyarta, kokarinta da yin tunanin irin wannan ganin ta ceto rayuwar marassa lafiya lafiya masu karamin karfi tare da yi mata addu’ar fatan alkhairi da samun ikon yin fiye da haka.
Daga karshe Hajiya Fatima Muhammadu Buhari tare da Manyan baki sun gabatar bada kayan tallafin ga marassa lafiya, Kuma wadanda suka amfana sun nuna farin cikinsu, godiya da addu’ar fatan alkhairi a gareta tare yin addu’a ga mahaifinta Shugaban kasa Muhammadu Buhari Allah bashi ikon ida mulkinsa cikin nasara tare da samar da zaman lafiya a cikin kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA

YANDA ZAMAN KOTUN MAHADI SHEHU DA MUSTAFA INUWA YA GUDANA A BABBAR KOTUN DUTSIN-MA Da misalin karfe 10:20 na safiyar yau Litinin, Alkalai uku sun...

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION.

PRESIDENT BUHARI RECEIVES FMR VP ARCH NAMADI SAMBO ON NIGER ELECTION. President Muhammadu Buhari receives the Former Vice President Arch Namadi Sambo on the Republic...

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE?

WACCE KOTU ZA A KAI MAHADI SHEHU GOBE? muazu hassan @ jaridar taskar labarai Gobe za a kai mahadi shehu Wanda yan sanda suka kawo daga Abuja...

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity

Group Seek To End Discrimination, Call For Unity By Bello Hamza, Abuja The group under the aegis of initiative for coalition and rights protection a not...
%d bloggers like this: