Advert
Home Sashen Hausa Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan...

Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan tambihi

Fatawar saki a fim: Shugabannin Kannywood sun yi wa Sheikh Bashir Alfurƙan tambihi

BIYU daga cikin jagororin masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood, Alhaji Sani Mu’azu da Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama, sun yi wa wani shehin malami tambihi kan fatawar da ya yi cewar idan jarumi ya furta saki a kan matar sa ta cikin fim to matar sa ta gida ma ta saku.

A wani guntun bidiyo na tsawon sakan 30 wanda ke yawo a soshiyal midiya, an ga Sheikh Dakta Bashir Aliyu Umar na Masallacin Alfurƙan da ke Kano ya na gabatar da wa’azi ga wani taron jama’a kan wani al’amari, sai ya bada misali da irin sakin da a kan yi a cikin fim ɗin Hausa.

Ya ce: “Ko yaushe na kan kawo wannan misalin a ‘yan wasan Hausa, ko? Mutum a cikin wasan Hausa ya ce an ɗaura masa aure, ya ce ya saki matan sa, wai shi ya na faɗan cewa – kuma fa ya na da mata – wai ya faɗa ya ce, ‘Matan nawa ma duk na sake su!’ Wai ya na nufin matan nasa na wasan Hausa. To na gasken sun tafi! Na gasken sun tafi, don ba a wasa da sha’anin aure.

“Wannan fatawar ta babban malamin ta tayar da muhawara a wurare daban-daban cikin soshiyal midiya, jama’a kowa na faɗin albarkacin bakin sa.

Sani Mu’azu (a hagu) da Hamisu Iyan-Tama

Da yawa sun ce ya kamata a ga sauran bidiyon don jin ko malamin ya kawo wasu hujjoji daga Alƙur’ani da Hadisi ko ijma’ar don inganta fatawar sa.

Mujallar Fim ta tuntuɓi manyan ‘yan fim da dama domin jin abin da za su ce kan wannan magana, amma da yawa sun noƙe a kan cewa ba su san hujjar da malamin ya dogara da ita ba.

Amma biyu daga cikin su sun yi magana, wato Alhaji Sani Mu’azu, wanda babban furodusa ne, jarumi, kuma tsohon shugaban ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Hausa (‘Motion Picture Practitioners Association of Nigeria’, MOPPAN).

Sani Mu’azu ya fara ne da yin tambaya, inda ya ce: “To wanda ya auri mace a fim fa?”

Ya ci gaba da cewa: “Ina ganin Malam ya yi tsauri a fahimtar harkar fim a nan. Mai yiwuwa saboda Hausawa kan kira aikin da sunan ‘wasan kwaikwayo’.

“Babu wasa a harkar fim. Sana’a ce wacce ba za ka yi fatawa a kan ta ba sai ka fahimce ta.

“Aure ibada ce bisa sunnah. Idan Malam zai alaƙanta abin da aka yi don faɗakarwa, to babu shakka wanda aka gani ya kashe mutum don faɗakarwa, shi ma Malam zai yanke masa hukuncin kisa.

“Ni ba malami ba ne, amma na san Allah SWT ya yi amfani da hankaka don ya yi dirama ta nuna wa ɗan’adam yadda zai binne ɗan’uwan sa.

“Allah SWT ya na amfani da niyyar mu ne a ko da yaushe. Don haka, Malam ya amince da niyyar mu ta faɗakarwa shi ma.

“Allah SWT ya yafe mana inda mu ke yin kurakurai, ya kuma ba mu ladar faɗakarwa inda ayyukan mu su ka wayar da kan mutane.”

Shi ma Hamisu Iyan-Tama da tambaya ya fara nasa tambihin, inda ya ce: “Idan har hakan ta tabbata gaskiya, to ina son Malam ya ba ni fatawa a kan idan kuma aka ɗaura aure, shi ma ya ɗauru?”

A wani saƙo da Iyan-Tama ya turo wa mujallar Fim, ya ci gaba da yi wa Sheikh Bashir tambayoyi kamar haka: “Idan mutum ya sha ruwa a matsayin giya (a fim) don nusarwa, shi ma giyar ya sha? Idan mutum ya rufe ƙofa da mace ya kashe fitala, shin zina ya yi turmi da taɓarya?

“Idan ɗan fim ya yi baccin wasa amma ba bacci ya yi da gaske ba, shi ma bacci ya yi? Idan ɗan fim ya fito a Kirista, ya na nufin ya zama Kirista kenan? Haka kuma idan Kirista ya fito a Musulmi, hakan na nufin ya musulunta kenan?”

Iyan-Tama, wanda furodusa ne, jarumi, kuma ɗan siyasa a Kano, ya ci gaba da ce wa shehin malamin: “Yanzu idan na fito a sheikh (a fim), ya na nufin ni na tabbata shehin malami? Idan na fito a shugaban ƙasa ko gwamna, hakan na nufin na tabbata ɗaya cikin biyun kenan?

“Idan na fito a matsayin Sheikh Dakta Bashir na Alfurƙan, hakan na nufin na zama shi kenan, da sauran misalai da dama?

“Kamar a fim ɗin ‘The Message’, Anthony Quinn ba Musulmi ba ne, amma ya fito a matsayin Sayyidina Hamza. Meye matsayin sa kenan?”

Iyan-Tama ya ce ya yi waɗannan tambayoyin ne domin ya na son ya ƙara ilmi don sanin yadda zai aiwatar da fim a nan gaba.

Wasu ‘yan fim kuma waɗanda wakilin mu ya kira a waya ba su ɗaga wayar ba.

Duk da haka, wasu ‘yan fim da su ka ce a sakaya sunan su sun ce ba su amince da wannan fatawar ta Sheikh Dakta Bashir ba.

Ba shakka, ‘yan fim na tsoron ja da malamin ne saboda batun ya shafi addini.

A fim ɗin ‘The Message’ wanda darakta Moustapha Akkad ya yi a 1976, jarumi Anthony Quinn, wanda ba Musulmi ba ne, ya fito a matsayin Sayyadina Hamza.

Munciro daga Mujallar Fim magazine dake busa yanar gizo

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Jam’iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa

Jam'iyyar PDP a Katsina ta sanar da kuɗin form ɗin takarar shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓe mai zuwa Babbar jam'iyyar adawa a jihar...

Aisha Buhari Ta Naɗa Kashim Shettima A Matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu Na Kwalejin Future Assured

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta naɗa Kashim Shettima, tsohon gwamnan Jihar Borno, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na Kwalejin Future Assured da ke...

WHICH PARTS OF NIGERIA ATTRACTED MORE FOREIGN INVESTMENTS IN THE YEAR 2021?

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/262020019347856/

AGAIN, A NEW ADDITION TO NIGERIA’S MARITIME SECURITY VESSELS!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/261866049363253/

Jami’an Hukumar yaƙi da yima Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annuti ta ICPC sunyi Dirar Mikiya jihar Katsina….

Jami'an Hukumar sun gano yadda akayi Haɗin baki da Ɗan Majalisar Wakilai da kuma Mai duba ƙwangila aka sace kuɗin ƙwangilar Naira Milyan Talatin...