Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin tsohon shugaban hukumar zaɓe, INEC, Farfesa Attahiru Jega, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na jam’iar Jos (UNIJOS).

Ministan ilimi, Adamu Adamu, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja, yace Buhari ya amince da naɗin shugabannin jami’o’in tarayya 42 dake faɗin ƙasar nan, kuma aikin nasu ya fara aiki nan take.

Shugaban ya kuma amince da naɗin biyu daga cikin tsofaffin ministocinsa, Prof Anthony Anwuka da Udoma Udo Udoma, a matsayin shugabannin majalisar zartarwa a wasu jami’o’i.

Yayinda da Anwuku zai jagoranci majalisar jami’ar albarkatun man fetur dake Effurum, jihar Delta, shi kuma Udoma zai jagoranci ta jami’ar Bayero dake Kano.

Hakanan kuma shugaba Buhari ya amince da naɗin shugabannin jami’o’i (Chancellors) mallakin gwamnatin tarayya. Adamu, yace:

“Kamar yadda mukasan iyayen mu sarakuna suke yi, muna fatan waɗannan shugabannin su zama masu kyautatawa jami’ar da aka tura su.” “An ɗauke su daga yankin da suke gudanar da mulkinsu zuwa wani wuri na daban kuma muna fatan waɗannan naɗe-naɗen zasu taka rawa wurin ƙara danƙon zumunci tsakanin al’ummar Najeriya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here