FARASHIN KAYAN AMFANIN GONA A KASUWAR BATSARI TA JIHAR KATSINA

Daga Misbahu Ahmad
@ jaridar taskar labarai.

Kasuwar Batsari babbar kasuwa ce wadda ke ci duk ranar alhamis, don haka ne ma muka ziyarci kasuwar a ranar alhamis 18-02-2021 inda muka samo farashin kayayyakin amfanin gona da kayan lambu, mun tattauna da Sarkin ma’aunan Sarkin Ruma.
Malam Ayuba mai awo, wanda shine ya bayyana mana yadda farashin yake, daga bisani kuma muka bi rumfa-rumfa domin tabbatar da yadda abun yake, ga kadan daga cikin farashin da muka samo;
1. Buhun masaranaira dubu ashirin (N20000).
2. Buhun dawa naira dubu goma sha shida da dari takwas (N16800).
3. Buhun gero naira dubu goma sha tara da dari biyu (N19200).
4. Buhun wake naira dubu talatin da daya (N31000).
5. Buhun waken suya naira dubu ashirin da takwas (N28000).
6. Buhun tsababbar gyada naira dubu talatin da takwas (N38000).
7. Buhun gyada shanshera naira dubu goma sha biyu (N12000).
8. Buhun farin rogo naira dubu goma sha takwas, akwai na naira dubu ashirin da biyu (N18000 da N22000).
9. Buhun aya naira dubu ashirin da takwas (N28000).
10. Buhun dankali naira dubu bakwai, akwai na naira dubu takwas da dari ukku (N7000 da N8300).
Sai kayan lambu, watau kayan cefane;
1.Buhun Tugande busasshe naira dubu ashirin da ukku (N23000).
2. Buhun Tugande danye naira dubu hudu da dari biyar, akwai na naira dubu bakwai (N4500 da N7000).
3. Kwandon tumatari naira dari takwas (N800).
4. Buhun tarigu naira dubu shida, akwai na naira dubu tara da dari biyar (N6000 da N9500).
5. Daurin albasa naira dari takwas (N800).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here