Farashin Burodi zai yi Tashin Gwauron Zabi da kashi Talatin cikin Ɗari….. Masu Gidajen Burodi

– Kungiyar masu gidajen burodi ta Nigeria, AMBCN, ta Sanar da ƙarin farashin burodi da sauran kayayaki kamar biskit da kashi 30 cikin 100

– Kungiyar, ta bakin shugabanta na ƙasa Mansur Umar ya ce karin ya zama dole ne duba da yadda filawa da sauran kayan hada burodi suka yi tsada a kasuwanni.

– Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Nigeria ta taimaka domin ganin an rage farashin kayayyaki musamman filawa da itace kanwa Uwar gami a harkar Sanaar su.

Kungiyar masu gidajen burodi ta Nigeria, AMBCN, ta umurci mambobinta a dukkan sassan ƙasar su kara farashin burodi, biskit da sauran kayayyakin da kashi 30 cikin 100 saboda mummunan halin da tattalin arzikin ƙasar ta shiga, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta yi bayanin cewa ta yi ƙarin farashin ne sakamakon ƙaruwar farashin kayayyakin hada burodi kamar sukari, bota, filawa, yist da sauransu.

Wannan umurnin na daga cikin matakan da aka cimma a ƙarshen taron shugabannin ƙungiyar da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mansur Umar, ya yi bayanin cewa: “Bayan la’akari da tashin gauron zabi da kayayakin hada burodi suka yi, domin tabbatar da cewa sana’ar mu bata durkushe ba, kungiyar ta yanke shawarar ƙara kudi da kashi 30 cikin 100.”

Kungiyar ta nuna rashin jin dadin ta bisa ƙarin farashin da ta ce yana tilasta wasu mambobinta dena sana’ar.

Yayin da ta ke kira ga mambobinta su kara farashi da kashi 30 domin tsadar kayayyakin aikinsu, AMBCN ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakan ganin an rage tsadar flawa da ke yi wa sana’arsu illa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here