#GaskiyarLamarinNijeriya  @do you know NG

Ko kun san cewa, a ranar 22 ga Yuli, 2021, Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amshi jiragen yaƙi ƙirar Super Tucano daga Ƙasar Amurka a matsayin ƙarashen jiragen da ta sayo, don cigaba da yaƙi da ta’addanci a Nijeriya?

Sayen jirgin yaƙi na Super Tucano na daga cikin irin shirye-shiryen da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen ganin ta shirya tsaf, don kawo ƙarshen ‘yan bindigar da suka addabi wasu sassa na ƙasar. Don haka ne ma ake ƙoƙarin ganin an tabbatar da ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

Shi dai jirgin yaƙin Super Tucano ba a yarda a yi amfani da shi ba sai a kan masu laifin da duniya ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, wato kamar Boko Haram, ISWAP da sauransu. Jirgin yaƙi ne na musamman kuma na zamani, wanda ya shahara a duniya wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.

Tanadar irin wannan jirgin yaƙi da Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi a daidai lokacin da ake batun ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ‘yan ta’adda, ya na nuni da cewa, baya ga yaƙi da Boko Haram da kuma ISWAP da Nijeriya za ta yi da Super Tucano, su ma waɗancan masu yi wa mutane kisan kiyashi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, za su ɗanɗana kuɗarsu ba da jimawa ba.

Wannan na daga cikin irin namijin ƙoƙarin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke yi wajen ganin ta samar wa Nijeriya da ‘yan Nijeriya kyakkyawar makoma, duk da irin ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here