Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa tafiyar da al’amurran siyasa cikin fahimta, kaunar juna da mutunta juna ne hanya daya tilo ta za ta jawo mutanen kirki su shigo kuma a samar da irin gaban da ake bukata ga kasa da al’ummar ta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a garin Gombe, cikin jawabin da ya gabatar a fadar Gwamnatin Jihar, a yayin da shi da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa suka wakilci kungiyar Gwamnonin da aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar APC (Progressive Governors Forum) domin jajanta ma Gwamnati da al’ummar jihar bisa rashin rayukan da akayi sakamakon wani yamutsin siyasa da aka samu a jihar kwanan baya.

Ya kara da cewa tashin hankali bai taba zama hanyar warware matsala ba ko samar da biyan bukata ba ko ci gaba.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar jihar dama sauran jihohi, musamman na jam’iyyar APC, da su rika daukar matakan da duk suka kamata domin tabbatar da ana yin siyasa ba da gaba ba, ballantana har a kai ga fadace fadacen da har zai kai ga rasa rayuka da dukiyoyi.

A karshe ya kuma roki Allah da ya gafarta ma wadanda suka rayukan su ta dalilin wannan hatsaniya da kuma sauran wadanda suka rasa rayukan su ta wasu ibtila’o’in musamman na ‘yan ta’adda.

Da yake maida jawabi, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya mika godiyar shi da ta al’ummar jihar Gomben bisa wannan ziyara ta jajantawa da aka kawo masu. A inda ya kara da cewa wannan hatsaniya hakika ba wanda tayi ma dadi hasali ma ta kara kunna wutar kiyayya ne a tsakanin al’umma. Ko da yake da yardar za a zauna da duk wadanda abin ya shafa domin a tattauna kuma a ba zukata hakuri domin a dunkule a hada karfi domin a gyara siyasar kuma a ciyar da Jihar gaba.

Daga cikin wadanda suka tarbi bakin, baya ga Gwamna Muhammad Inuwa, akwai Mataimakin shi Manasseh Daniel Jatau, Shugaban Majalisar Sarakuna ta jihar Mai-Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad da kuma wasu manyan jami’an Gwamnatin jihar ta Gombe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here