Daga Shafin AbdulHadi Ahmad Bawa

Abinda ke tada mani hankali shi ne, da yawa ‘yan PDPn basu dauki wannan darasi ba ballantana su amfana dashi, haka muma dake APCn da yawan mu bamu koyi komi ba daga faduwar PDPn ballantana kuma nasarar da muka samun.

Mu kiyayi yankan hukunci daga nesa da kuma shaidar zur.

Ba don dorewar siyasa ba, a’a, don fita hakkin al’umma da dora ta bisa hanyar da za ta zamo mafita gare mu baki daya, lokaci yayi da zamu zauna muyi nazari tare da amfani da wadancan darussa.

Wannan shawara ce gare mu baki daya; mu da muka ce mun ji mun gani sai mun yi siyasa.

Akwai yiwuwar wasu su kasa fahimtar inda na dosa, amma tabbas duk wanda abin ya shafa kai tsaye, da ya karanta zai gane.

Ya Allah Kasa mu wanye lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here