WATA SABUWA: Fadar Shugaban Kasa Ta Fara Nazarin Sake Rufe Iyakokin Najeriya
Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta sanar cewa ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar da ta bude kwanan nan a sakamakon yadda ’yan ta’adda da kananan makamai ke kwararo wa cikin kasar.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da hakan yayin hirar da ya yi a wani shiri na Sunrise Daily wanda gidan talbijin na Channels ya saba haska wa.
Gwamnatin ta ce tana ci gaba da nazari a kan al’amuran da suke faruwa cikin al’ummomin da ke kan iyaka da kasar Najeriya, lamarin da ta ce da yiwuwar za ta rufe iyakokin na ta muddin aka ci gaba da samun tangarda.
Mallam Garba ya ce Gwamnatin Najeriya ta lura cewa kasashen da ke makwabtaka da ita ba su ba da hadin kai ba wajen dakile kwararowar ’yan ta’adda da kuma kananan makamai, wanda a cewarta hakan na kara rura wutar ta’addanci a kasar.
Ya bayyana cewa, “Wannan shi ne dalilin da ya sanya Shugaban Kasa tun a wancan lokaci ya yanke shawarar rufe iyakokin kasar har zuwa yanzu da aka bude su a makon jiya.
“Muna ci gaba da tattauna wa da makwabtanmu domin su bayar da hadin kai wajen ganin an dakatar da kwararowar ’yan ta’adda, makamai, muggan kwayoyi da yin fataucin mata amma lamarin ya ci tura sabanin tsammanin da shugaban kasar ya yi.
“Wannan shi ne dalilin da ya tilasta shugaban kasar na ba da umarnin rufe iyakokin kasar.