Home Sashen Hausa EndSARS: An kai ƙarar gwamnatin Najeriya kotun duniya

EndSARS: An kai ƙarar gwamnatin Najeriya kotun duniya

EndSARS: An kai ƙarar gwamnatin Najeriya kotun duniya
Shugaba Buhari

Ƙungiyar da ke sa ido kan ayyukan gwamnati a Najeriya mai suna Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kai ƙarar gwamnatin Najeriya wurin mai shigar da ƙara a kotun hukunta manyan laifuka.

Ƙungiyar na neman kotun ta binciki rahotannin da ke cewa “jami’an tsaro da ‘yan siyasa sun yi amfani da ‘yan daba domin cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS a Abuja da Legas da Osun da Kano”.

SERAP ta roƙi Fatou Bensouda ta ƙoƙarta wurin “tabbatar da cewa an gurfanar da masu laifi waɗanda akasarinsu jami’an gwamnati ne da sojoji da ‘yan siyasa da suka shiga lamarin kai-tsaye ko ta hanyar wakilci”.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce an kashe aƙalla ‘yan zanga-zangar EndSARS 38 a faɗin Najeriya, inda aka kashe mutum 12 a Legas ranar Talata bayan sojoji sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai na hannunmu - DSS Rundunar 'yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa...

Ansako ɗaliban makarantar Kagara da aka sace

GSC Kagara: An sako mutum 41 da aka sace a makarantar Kagara ta Jihar Neja An sako ɗaliban makarantar Kagara da malamansu da ma'aikata guda...

PRESS RELEASE ; GANDUJE SACKS MEDIA AIDE

PRESS RELEASE GANDUJE SACKS MEDIA AIDE Governor Abdullahi Umar Ganduje of Kano state has relieved his Special Adviser on Media, Salihu Tanko Yakasai of his appointment...

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 26/02/2021 7 DAYS ACHIEVEMENTS OF CP SAMA'ILA SHU'AIBU DIKKO, fsi IN KANO STATE ... As 9 Kidnapping Suspects, 8 Armed Robbery...

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar..

Bamu da Adalci, Dole ne mu cire batun Siyasa idan ba Haka ba Muna gidajenmu zamu Hallaka ~Inji Atiku Abubakar.. Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku...
%d bloggers like this: