Advert
Home Sashen Hausa EndSars: Abu shida da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi...

EndSars: Abu shida da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya kan zanga-zangar

EndSars: Abu shida da Buhari ya faɗa a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya kan zanga-zangar

Shugaba Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya

Bayan shafe kwana da kwanaki ana jiran martanin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari dangane da zanga-zangar nuna adawa da zaluncin da ake zargin ‘yan sandan kasar na yi, daga karshe dai ya ɓara.

Shugaban kasar ya gabatar da jawabi, da aka naɗa ta bidiyo in da ya tattauna batutuwa da dama, kama daga kan zanga-zangar ta EndSARS, da kuma sauran matsalolin da kasar ke fuskanta a yanzu.

Ga wasu daga cikin muhimman batutuwa biyar da ya yi tsokaci a kansu, yayin jawabin na sa.

1. Damar zanga-zanga

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince kan cewa ba shakka al’ummar kasar na da damar yin zanga-zanga kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya basu dama, sai dai sashen ya buƙaci a kiyaye doka a kuma kauce wa shiga hakkin jama’a.

Ya ce su kansu matasan da suka fito suna zanga-zangar EndSARS da farko sun yi ta ne cikin lumana, kafin daga bisani wasu ɓata gari suka fake da ita wajen haifar da yamutsi da tayar da hankalin jama’a, da kuma ƙona gine gine da ƙadarorin gwamnati.

Ya bayar da misalin fadar mai martaba Oba na Legas da ɓata gari suka kai wa hari, da kuma kutsa wa filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa da ke Legas da suka yi.

2. Ba za mu amince da tayar da zaune tsaye ba

To sa dai a cewar Shugaba Muhammadu Buhari, duk da sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya bai wa ‘yan kasa damar yin zanga-zanga, ya kuma yi gargaɗi a kan tayar da yamutsi da sunanta.

”Babu ta yadda za mu amince da tayar da zaune tsaye, mun ji kokenku yadda ya kamata, muna kuma ɗaukar matakai a kansu.

Shugaban ya kuma yi kira ga ‘yan kasar su koma harkokinsu, bisa alkawarin cewa jami’an tsaro za su ci gaba da ƙoƙarin kare lafiya da dukiyoyinsu musamman ‘yan sanda.

3. Walwalar ƴan sanda

Dangane da walwalar ‘yan sanda, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai don tabbatar da walwalarsu, ta yadda za su kiyaye rayukan jama’a yadda ya kamata.

”Mun bai wa hukumar kula da albashi umarnin sake nazartar albashin ‘yan sanda, har ma da sauran hukumomin da suka hadar da na hukumar kashe gobara.

Gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ta yadda za su koma harkokinsu ba tare da wata fargaba ba.

4. Yaƙi da talauci

Shugaban ya bayyana cewa babu wata gwamnati a Najeriya da ta ɗauki gabarar yaƙi da talauci ta hanyar bijiro da matakai daban-daban na magance su kamar tasa, don haka ya kamata masu zanga-zangar su lura cewa da gaske suke wajen shawo kan matsalolin da suka shafi matasan Najeriya.

Ya lissafo wasu shirye-shirye da gwamnatinsa ta bijiro da su da tuni suka fara aiki domin rage talauci a tsakanin ‘yan Najeriya.

Wasu daga cikinsu da ya lissafo sun haɗar da :-

  • Farmermoni,
  • Tradermoni,
  • Marketmoni,
  • N-Power,
  • N-Tech and
  • N-Agro.

5. Takaicin rasa rayuka da gargaɗi kan yaɗa karya game da gwamnati

”An yi ta’adi sosai duk da sunan zanga-zangar EndSars. Na ji matuƙar taƙaici kan irin asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi. Waɗannan masifun ba su dace ba. Bai kamata a aikata irin waɗannan abubuwa da sunan bayyana takaicin da matasan ƙsarmu ke ciki ba.

”Sannan irin yadda ake yaɗa labaran ƙarya a shafukan sada zumunta da sunan cewa wannan gwamnatin nan ba ta damu da halin da ƴan ƙasarta ke ciki ba, tuggu ne na son karkatar da hankalin mutane a ciki da wajen ƙasar wajen yi wa gwamnatin rashin adalci,” in ji shugaban.

6. Martani ga kasashen duniya

Shugaban bai gushe ba, sai dai ya yi magana dangane da kasashen duniya da suka yi Allah wadai dangane bude wa masu zanga-zanga wuta da sojoji suka yi, in da yace kamata ya yi su nemi ƙarin bayani ko kuma neman ainihin hujjar abin da ya faru, maimakon dogara da ɓangare guda.

”Muna gode wa dukkanin wadanda suka bayyana damuwa dangane da wannan batu, muna kuma ɗaukar matakai a kansu, amma yana da kyau a rika tuntuɓa kafin ɗaukar matsaya,” in ji Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

LADY FROM KATSINA REACHED EVANGELICAL COUNCIL

from Catholic daily star @ katsina city news The first indigenous Hausa lady in Nigeria to make Perpetual Vows of the Evangelical Councils in the Dominican...

RECONCILIATION HITS BRICK WALL IN KATSINA PDP ___LAWAL RUFA’I SAFANA

Hassan Male @ www.katsinacitynews.com Negotiations to mend the cracks within Peoples Democratic Party PDP in Katsina State have ended in dead lock as conflicting parties failed...

TRADITIONAL RULER ADVOCATES FOR MORE CONCERTED ENLIGHTENMENT AGAINST CHOLERA OUTBREAK

TRADITIONAL RULER ADVOCATES FOR MORE CONCERTED ENLIGHTENMENT AGAINST CHOLERA OUTBREAK Hassan Male Alhaji Usman Bello Kankara the Kanwan Katsina district head of Ketare has admonished the...

BASARAKE YAYI KIRA DA A DAGE WAJEN WAYAR DA KAN AL’UMMA AKAN ILLOLIN CUTAR AMAI DA GUDAWA

  Hassan Male Alh. Usman Bello Kankara (UK Bello) Kanwan Katsina hakimin Ketare yayi kira ga magaddan gundumarsa, limamai da sauran shugabannin al'umma da su himmatu...

Late M.D Yusuf’s Youth Empowerment Legacy in Katsina

Late M.D Yusuf’s Youth Empowerment Legacy in Katsina Francis Sardauna writes that the Empowerment of 11,901 vulnerable people at the Katsina Vocational Training Centre will contribute...
%d bloggers like this: