EndSARS: Ƙungiyar da ta shirya zanga-zangar ta ce a haƙura a zauna a gida

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafukan zumunta, ƙungiyar ta ce ba za ta sake karɓar wata gudummawar kuɗi ba da sunan EndSARS sannan ta buƙaci matasan da su bi dokar hana fita da aka saka a wasu jihohi.
Ana kallon sanarwar a matsayin abin da ka iya kawo ƙarshen jerin gwanon da matasa suka shafe mako biyu suna yi a tituna wanda kuma ya rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu jihohi kamar Legas da Edo.
Sanarwar na zuwa ne awa biyar bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci matasa su dakatar da zanga-zangar, yana mai cewa cigaba da yinta “zai jawo wa tsaron ƙasa cikas kuma abin da ba za a amince da shi ba ne”.
Ƙungiyar ta ce ta tara kusan dalar Amurka 400,000 na gudummawa daga sassan duniya, wadda har yanzu ba a kashe akasarinsu ba.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce jami’ansa sun gana da Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ranar Alhamis domin bayyana masa damuwarsu.