YANZU-YANZU: Gwamna El-rufa’i Ya Bawa ‘Yan Unguwar Makarfi Da Rigasa Awa 72

Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i, ya bawa ‘yan unguwar Makarfi da Rigasa wa’adin awa 72 su tattare yanasu-yanasu su fece daga Unguwar.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki biyar da rushe gidaje a unguwar Malali Low-cost.

Al’ummar gari dai na ci gaba da Allah wadai da wannan rusau da Gwamnatin jihar Kaduna ke yi da sunan gyara, dayawan mutane sun rasa muhallin da zasu ci gaba da rayuwa.

Me zaku ce game da rusau da Gwamnatin Jihar Kaduna ke yi da sunan gyara?

– Daga Jaridar Arewa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here