Elon Musk ya zama mutumin da ya fi kowa kudi a duniya da dala biliyan 185

Attajirin nan Elon Musk, mai kamfanin Tesla da SpaceX ya zama na ɗaya cikin jerin attajiran duniya bayan hannun jarin kamfanin Tesla ya ƙaru a ranar Alhamis.
Ya maye gurbin mai kamfanin Amazon Jeff Bezos, wanda ya fi kowa kudi a duniya tun 2017.
Darajar kamfanin Tesla da ke ƙera motocin lataroni na Elon Musk ta ƙaru a bana, kuma darajarsa a kasuwa ta kai dala biliyan 700.
Hakan ya sa kamfanin na motoci ya zarta Toyota da Volkswagen da Hyundai da GM da kuma Ford idan an hada su baki daya.