El-Rufai ya yi wa ‘yan gidan yari 12 afuwa

Nasir Elrufai

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayar da umarnin sakin mutum 12 daga gidan yari.

Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai ya fitar ta ce mutanen sun ƙunshi 10 da aka yanke wa hukuncin zaman shekara uku ko fiye, inda ya rage musu saura wata shida ko ƙasa da haka.

Muyiwa Adekeye ya ce an saki sauran mutum biyun ne sakamakon yawan shekarunsu.

“An ɗaure Gabriel Olugbenga tsawon shekara bakwai bisa laifin kisa a shekarar 2016. Shekararsa 60 kuma saura wata shida ya kammala zaman gidan yarin, wanda ya kamata ya gama a Yunin 2021,” in ji shi.

“An ɗaure Tunde Ikuenaya shekara huɗu a watan Nuwamba na 2017. Shekararsa 64 kuma ana sa ran sai Maris 2021 zai kammala zaman gidan yarin.”

Kazalika, El-Rufai ya rage adadin hukuncin da aka yanke wa wasu mutum uku zuwa shekara biyar “saboda sun yi zaman shekara 10 ko fiye kuma sun nuna ɗa’a”.

‘’Ifeanyi Chiebuike Nweke da Mohammed Mamman Santare da Samaila Danjuma, an yanke musu hukunci ne a lokuta daban-daban sakamakon laifin kisa.”

Nasir El-Rufai ya yi musu afuwar ne a matsayinsa na gwamnan Jihar Kaduna, kamar yadda sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ba shi dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here