… Manyan Ma’aikata Kuwa Za’a Ba Su Kyautar Kashi 30 Na Albashinsu

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amince da biyan alawus-alawus na karshen shekara ga ma’aikatan gwamnati a jihar.

Za’a bayar da alawus-alawus ɗin ne a karshen wannan wata na Disamba, inda za a biya ƙananan ma’aikata kashi 100 na albashinsu, yayinda su kuwa manyan ma’aikata za su samu kashi 30% na albashin su na wata.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin Kaduna mai ɗauke da sa hannun Kakakin gwamnan, Muyiwa Adekeye, inda ta bayyana cewa alawus-alawus din na ƙarshen shekara na daga cikin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi domin kyautata jin dadin ma’aikatan gwamnatin jihar tare da ƙara musu ƙwarin gwiwa ta fuskar gudanar da aikinsu.

Kamar yadda tsarin ya nuna , za’a biya ma’aikata daga mataki na 1-7 kashi 100% na albashinsu na wata-wata a matsayin ƙarin shekara – shekara.

A dayan bangaren kuma ma’aikatan gwamnati daga mataki na 8-13 za su samu kashi 40%, yayin da manyan jami’an da ke mataki na 14 zuwa sama za su karbi kashi 30% na albashinsu.

Gwamnatin ta ce ta ware Naira biliyan 1.38bn wanda tsarin zai laƙume ga ma’aikatan jihar.

A watan Satumban shekarar 2019, gwamnatin jihar Kaduna ce ta zama gwamnati ta farko a faɗin Najeriya da ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi. Haka zalika jihar ta kuma ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N30,000 duk wata ga wadanda suka yi ritaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here