EFCC ta kwato karin $153m daga wurin Diezani

Diezani

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta sanar da kwato $153m daga hannun tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke wadda ta tsere daga kasar zuwa Birtaniya a 2015.

Jaridar Vanguardta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun kwace akalla kadarori 80 da kudinsu ya kai $80m.

“Muna fatan ganin lokacin da, watakila, za ta shigo kasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu dauka nan gaba. Tabbas ba mu yi watsi da batunta ba,” a cewar Abdulrasheed Bawa.

Ya shaida wa manema labarai cewa a shirye yake ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin hukumar EFCC “idan wani ya sa na yi abin da bai dace ba”.

Ms Alison-Madueke ita ce ministar man fetur daga2010 zuwa 2015.

Ta musanta aikata ba daidai ba lokacin da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya yi zargin cewa $20bn na man fetur sun bata a karkashin shugabancinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here