EFCC Ta Chafke Uwar-Gidan Gwamnan Jihar Kano, Hafsat Ganduje

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati, EFCC, ta kama uwar gidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja.

Hafsat Ganduje, wacce babban ɗanta ya shigar da ƙorafi a kanta, an gayyace ta don yi mata tambayoyi amma aka tsare ta a ranar Litinin da daddare, watakila don ci gaba da binciken tane da safiyar Talata, kamay yadda kafar Daily Star Nigeria ta ruwaito.

Idan ba’a manta ba babban ɗan gwamnan jihar Kano, Abdul’Azeez Umar Ganduje ne ya yi wa mahaifiyar tasa cune a hukumar EFCC bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe, daga bisani ya kwashi iyalinsa zuwa ƙasar Masar (Egypt).

Mun yi ƙoƙarin ji daga wasu muƙarraban gwamnan amma hakan ya ci tura har izuwa lokacin haɗa wannan rahoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here