Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa Gwamnatin Jiha, duk da kalubale daban daban da take fuskanta, za ta ci gaba da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar ta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan da ya gama duba ayyukan wasu hanyoyi guda hudu da Gwamnatin Jihar Katsina take kai.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa yana sane da duk alkawurran dake tsakanin shi da al’ummar jihar Katsina, kuma yana kan cika su daidai da yadda yanayi bada kuma iyakar iyawar shi tsakanin shi da Allah.

Hanyar farko da aka duba ita ce wadda ta tashi daga Gurjiya zuwa Karkarku taje Kwasarawa ta bulle Sandamu, Mai tsawon kilomita Goma sha Daya da dugo Biyu (11.2km). Wannan aiki yayi nisa kwarai kamar yadda Kwamishinan Ayyuka Alhaji Tasi’u Dandagoro ya bayyana cewa, an kammala kashi Chasa’in da biyar bisa Dari.

Hanya ta biyu ita ce wadda ta tashi daga Rogogo zuwa Zango mai tsawon kilomita Ashirin (20km), wadda tsananin lalacewar ke jawo matsaloli da dama ga matafiya ga kuma durkusar da tattalin arzikin yankin. Wannan yasa Gwamnatin Jiha ta bada aikin gyaran wannan hanya tare da shimfida mata dallof. Shi ma wannan aiki Alhamdu lillah, ya mika, kuma yana tafiya cikin inganci.

Hanya ta ukku da Gwamna ya duba ta tashi ne daga Bumbum zuwa Kasanki daga nan ta gangaro Majigiri ta iso Dankama wadda ita ma ake gyaran ta.

Wannan hanya an gina ta tsakanin 2011 da 2015, kuma a ta bakin Kwamishinan Ayyuka, bayanin da kuma Injiniya Murtala Mani, wakilin Dan kwangilar ya tabbatar, tun farkon aikin ba ayi shi da inganci ba, wanda hakan yasa cikin dan karamin lokaci hanyar ta fita hayyacin ta. Yanzu akwai kilomita goma da sai an kankare su gaba daya kana ayi sabon zubi da dabe kana akai ga sa kwalta.

Hanya ta hudu kuma ta karshe a jerin hanyoyin da aka duba ita ce wadda ta tashi daga Katsina taje Kaita ta wuce Dankama.

Ita wannan hanya dadadda ce mai dallof. Matsalar da ta fuskanta ita ce ta zaizayewar gadoji da kwalbatoci a daminar bara, haka kuma fadinta mita Shidda ne daidai, mamadin mita bakwai da dugo ukku, awon da ake amfani dashi a ko ina. Haka kuma za a zizara mata wurin fakin (shoulder) a gefen hagu da dama, Mai fadin mita daya da rabi ko wanne.

Akwai hanyoyi guda biyu da aka fara aikin su, amma matsalar tsaro ta tikasta an dakatar dasu, su ne ta Gurbin Baure zuwa Shimfuda ta isa Batsari sai kuma wadda ta tashi daga Kankara zuwa Dansabau zuwa iyakar mu da Jihar Zamfara.

Haka kuma, Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa akwai hanyoyin da aka kammala shirye shiryen bada ayyukan su amma matsalar rashin tsaro ta hana a bada ayyukan su. Wadannan hanyoyi su ne; Birchi zuwa Wurma zuwa Batsari da kuma ta Danmusa zuwa Maidabino ta bulla Kankara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here