Duk Wanda Ya Mari Matarsa, Ba Ya Mari Banza Ba Ne; Ya Kamata A Rama Ma Ta. -In ji Shaikh Yakubu Yahaya Katsina.

Daga A.I Musa

Shehin Malamin Islaman, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da Tafsirin alkur’ani mai girma na watan Ramadan a ranar Asabar din nan.

Malamin ya ce, Manzon Allah (S) ya hana a Mari ko da fuskar Dabba ce, balle ta dan Adam, balle kuma ta Matar da Mutum ke Aure.

“Wasu kuma fuskar Mata suke Mari; Katsam! Wanda duk ya Mari Matarshi, ba fa ya Mari haka nan ba ne ba, ba ya Mari banza ba ne; ya kamata a rama ma ta!” Ya nusar.

Ya ci gaba da cewa, “Ko Fatarta ta tashi; ko ta yi Ja; ko Idonta Ya yi Ja (in ya bige ta); sai ya biya Diyya, ko ya ba da a rama ma ta.” In ji shi

“In da Bulala ka bige ta, a samu Bulala a ba ta, kai ma ta zane ka. In ka ji ma ta rauni; a ji ma ka rauni. In ma fidda ma ta jini; ka biya Jinin. In ba ka biya a duniya ba, Lahira za ka biya in ka nuna fin karfi.” Ya tsoratar.

“Wa ya taɓa jin a ciki Tarihi Manzon Allah(S) ya taɓa nuna matar sa da yatsa? Wa ya taɓa jin wani Imami a cikin A’immatu Ahlulbaiti ya taɓa nuna matar sa da yatsa ballantana mari? To wa taɓa jin an ruwaito zagi?” Ya tambaya.

Shehin Malamin ya an karar Mazaje cewa, idan Mutum ya auri Mace; ba yana nufin an aura ma sa Ruhinta da komai nata don ya azabtar da ita ba ne, a’a an aura ma sa ita ne don su yi taimakekeniya wajen bin Allah (T) ne.

Malamin ya haskaka wa Mazaje cewa, duk da yake Mata su kan yi abin Mari ko duka, amma hakan ba gazawa ko gangancinsu ba ne; dabi’arsu ce wadda Allah(T) da ma ya halicce su da ita.

Bugu da kari, Malamin ya kuma gargadi wasu Mazaje masu hana matansu a binci a matsayin daukar fansa kan wani laifi da suka yi ma su a zamantakewarsu ta aure, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye wa matayen nasu hakki.

“Ko kuma(Miji) ya dauki fansa ya hana(Matarsa) abinci. Wai ya dauki fansa ya hana matarsa abinci…Manzon Allah ya ce (su Mata) “Fursunoni ne a hannunku.” Ba fursuna na laifi ba, an siffanta su kamar fursunoni ne. In ka hana fursuna abinci, ka yi mugun laifi, ka tauye ma sa hakki. Ina zai je ya samo? Wajen wa?” Ya tambaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here