Advert
Home Sashen Hausa Duk wanda ya dauki Ganduje jagora sai yayi asara -Danbilki kwamanda-

Duk wanda ya dauki Ganduje jagora sai yayi asara -Danbilki kwamanda-

Wallahi duk wanda ya dauki Ganduje jagoransa yayi asara, nidai nayi nadama ~ Kwamanda

Jagoran Arewa Media Group, shugaban APC Akida, gatan funakaye Alhaji Abdulmajid Danbilki Kwamanda, yace yayi nadamar tallan gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da yayi a baya, kuma wallahi duk wanda ya dauki Ganduje jagoransa a siyasa to yayi asara, domin Ganduje mutum ne wanda ya kware a butulci, indai ka taimake shi to wallahi sai yayi maka fitsari a shinfida, don duk duniya ba wanda yayi masa gata a siyasa kamar Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, amma saida ya cije yayi masa fitsari a shinfida, kuma yace baya fatan Allah ya kara hada shi siyasa daya da Ganduje.

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, Kwamanda ya bayyana haka ne a daren yau yayin tattaunawarsa da gidan rediyon Nasara FM dake Kano, inda yace lokaci yayi da jam’iyyar APC a jihar Kano zata gyaru, tunda tabar hannun yan jari hujja, kuma ya kamata uwar jam’iyyar ta kasa ta zabi daya, domin bazai yiwu a zauna da shugabanci biyu a jiha ba, kuma yace tsarinsu na mutunta kowa ne, hatta yan Kwankwasiyya yana kiransu da suzo su shigo ayi tafiyar Sanata Barau Jibril Maliya, domin ya zama gwamnan Kano a 2023, duba da yadda yanzu bashi da sa’a a wajen taimakon talakawa, tallafi da jika hantar yan jam’iyya, ya kuma bukaci a cire maganar jam’iyya, a dinga duba cancanta.

Barau Jibril ya bayyana takaicinsa akan munafukan yan siyasa, irin wasu mutane a Kano da suke amsa sunan PDP suna zuwa wajen gwamnati suna cutar da jam’iyyarsu saboda tsabar rashin sanin kansu, ya kuma yi martani akan wani dan majalisa da yace idan Ganduje ya bashi dama zai ci mutuncinsu Shekarau da Barau, Kwamanda yace shi dan Santsi ne, wallahi sun amsa goron gayyata, zasu nuna masa shi karamin mara kunya ne, kuma daga wannan karan wallahi sai an kayar dashi, ko goya shi gwamna zaiyi.

Har ila yau, Kwamanda yace ai maganar da Ganduje yake da cewa su Shekarau da Barau suna Abuja suna karbe-karbe, ai gwano ne da baya jin warin jikinsa, domin shi ne jagoran yan karbe-karbe, da ake bashi dollar yana sawa a Aljihu, har dansa yakai karar matarsa zuwa EFCC, abinda yace bai taba ganin irinsa ba a tarihi, ga kuma yadda ake karbar kudaden yan kasuwa suna zurarewa a Aljihu, shi yasa kullum talakawa suke gudunsa.

Daga: Kano Online News
17/10/2021

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...