Duk Makarantun Firamare Da Sakandiren Jihar Katsina Ba Wadda Za Ka Shiga Kace Makaranta Ce, Balle Kujerun Zama A 2015

Gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello Masari

..Ga kudin dake zuwa daga Abuja sun fara karewa ko kuma suna gaf da karewa

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa a lokacin da jam’iyyar APC ta amshi mulki a jihar Katsina, duk illahirin makarantun firamare da sakandiren jihar nan, babu ko daya da za ka shiga ka ce makaranta ce ko kuma ka samu kujerun zaman a kaf din jihar Katsina.

Gwamna Aminu Bello ya bayyana Haka haka a lokacin da yake jawabi a karamar hukumar Danja a bikin wasu yan karamar hukumar da suka yi fice a wuraren aikin su daban-daban a jiya Asabar.

Masari ya kara da cewa aikin ba karami ba ne ba kuma na wasa ba ne, ba kuma ajin da za ka ce ba ka iske yara fiye da dari a aji guda ba matsalar da muka samu kenan a Kasa. Mun kafa kwamitin ilimi karkashin Badamasi Lawal Charanchi, da suka zagaya a wancan lokacin yaran da suka samu dubu dari da saba’in da wani abu, amma a rijistar akwai Miliyan daya da dubu dari.

Amma a yau a jihar Katsina muna da yara a firamare aji daya zuwa shidda miliyan daya da dubu dari Takwas, kuma har yanzu akwai wadanda ba su samu damar shiga Makarantar ba, idan wurare wadatattu za’a samu yara sama da miliyan ukku da za su shiga firamare a Katsina. Amma akwai matsalar azuzuwan da karancin Malaman da kuma abun Zama. Ga shi hanyoyin da ake samun kudin, sun yi karanci, saboda an shagwabar da mutanen cewa ai kudi za su zo daga Abuja, kudin dake zuwa daga Abuja sun fara karewa ko kuma suna gaf da karewa.

Masari ya ci gaba da cewa halin da Najeriya take ciki a yanzu, dole sai mun ga abinda za mu iya yi wa kanmu, a karamar hukumar Danja akwai arziki akwai wadata, domin akwai gona da ruwa da kuma jamaa. Ya kamata Mutane a tashi tsaye mu zama masu dogaro da kai. Kuma za mu ci gaba da yin duk abinda ya dace na inganta rayuwar al’umma jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here