Duk Gwamnan Dake Son Jiharsa Ta Zauna Lafiya Ya Koma APC – Gwamna Matawalle

Gwamnan jihar zamfara Bello Matawalle ya jaddada dalilin sa na barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnan a Wata hira da gidan talabijin na TOS ya yi da shi ya bayyana cewa ya yi kaura daga PDP din ne zuwa APC saboda yawaitar kashe – kashe da ake samu a jahar sa.

Ya yi kira ga sauran gwamnonin da Jahar su ke fama da matsalar rashin tsaro da su gaggauta komawa jam’iyyar APC mai rinjaye domin samun wanzuwar zaman lafiya a jahohin su.

Ya ce “Na yanke shawarar chanja jam’iyya ne saboda na kawo zaman lafiya a jaha ta, yanzu da duk muka kasance ‘yan jam’iyya daya zan samu cikakken goyan bayan gwamnatin tarayya domin kawo karshen rashin zaman lafiya a Jahar zamfara.

Majiya: Prime Time News Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here