Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kallon ƙwallon kafa da Najeriya za ta fafata da Ghana a Abuja a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a Qatar, in ji BBC Hausa.

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta gano cewa Buhari ya je kallon ƙwallon ƙafar ne yayin da ƙasar ke alhinin harin da ƴan ta’adda su ka kai wa jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna a jiya Litinin.

BBC Hausa ta rawaito cewa titin da ya fito daga fadar shugaban ƙasar har zuwa filin ƙwallon kafa da ke birnin Abuja ya kasance shiru babu ababen hawa saboda wucewar shugaban.

Gwamnati ta samar da tikitin shiga kallon wasan kyauta ga ƴan Najeriya domin nuna goyon baya ga ƴan wasan Najeriya.

Duk ƙasar da aka ci tsakanin Najeriya da Ghana ba za ta tafi gasar cin kofin duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here