Maigirma Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana haka ne yau a ofis din shi, lokacin da Arch. Faisal Jafar Rafindadi shugaban gasar zaluko matasa masu fasaha da gwamnatin jihar Katsina ke daukar nauyi, ya kawo mashi ziyara domin gabatar da wadansu matasa guda biyu da suka yi zara cikin wannan gasa.

Matashi na farko, Abdulhakim Bashir Gafai kasar Burtaniya (England) ta gayyace shi domin yaje ya nuna masu irin fasahar da yake da ita, sai kuma Anas Abdullahi Makera daga karamar hukumar Dutsinma wanda ya zana mota da mashin na noma, shuka, huda da kuma feshin maganin kwari.

Maigirma Gwamna ya kara da cewa gwamnatin jihar Katsina a shirye take domin taba matasa masu fasaha kwarin guiwa tare da goyon baya domin tabbatar da sun ci ribar fasahar tasu.

Abdulhakim Bashir ya gabatar wa Gwamnan da mashin din da ya kirkira wanda zai koya ma mahajjata yadda ake aikin hajji da kuma wata manhaja wadda za ta iya gane mai laifi wato (Ciniki Guard).

Domin tabbatar da ya sami kula da jagoranci mai kyau zuwa kasar Birtaniya, Gwamna Masari ya hada Abdulhakim da Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim Fantami, ya kuma yi mashi addu’a da fatar alkhairi a kan wannan tafiya da zai yi.

Shi kuwa Anas Abdullahi Makera, Gwamnatin Jiha za ta dauki nauyin kera mashin guda daya na noma, bisa zanen da ya gabatar wa Gwamnan, wanda yin hakan zai tabbatar da fasahar a zahiri.

Haka kuma, Maigirma Gwamna ya ba Anas Abdullahi Makera kyautar na’ura mai kwakwalwa ta tafi da gidanka (laptop).

Daga karshe, Gwamnan ya yaba ma matasan kwarai a bisa yadda suka jajirce har sukayi irin wannan tunani da zai amfane su ya kuma amfani jihar Katsina dama kasar baki daya.

Rahoto
Daga ofis din Darakta Janar Soshiyal Mediya na mai girma Gwamnan jihar Katsina.
21/12/2021 .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here