Advert
Home Sashen Hausa "Duk Ɗan Takarar da bai aje Aikin sa ba kuma ya fito...

“Duk Ɗan Takarar da bai aje Aikin sa ba kuma ya fito Zaɓe ya Ci, kamar Yayi Sallah ba Al’wala ne”……Barasta Ahamed Ɗanbaba

“Duk Ɗan Takarar da bai aje Aikin sa ba kuma ya fito Zaɓe ya Ci, kamar Yayi Sallah ba Al’wala ne……Barasta Ahamed Ɗanbaba.”

……..Ma’aikacin Gwamnati yanada dama ya shiga Siyasa

Barasta Ahamed Ɗanbaba Lauya Mai Zaman kansa a Katsina

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Barasta Ahamed Ɗanbaba Lauya ne mai zaman kansa da ya kwashe shekaru Talatin da biyu a kan Aikin Lauya da kare haƙƙin marasa galihu a Mai Dangana Chamber Katsina. A Zantawarsa da Jaridun Katsina City News yayi fashin baƙi akan Dokar zaɓe da kuma damar da ma’aikatan Gwamnati suke da ita ta shiga Siyasa ko goyawa wani ɗan takara baya.

“A tsarin Doka, duk ɗan Takara dole ne ya aje Muƙamin sa wata ɗaya kafin zaɓen fidda ɗan takara, idan kuma bai aje ba, ya fito zaɓe ya ci kamar yayi Sallah ne babu al’wala. Saboda ba zai yiyu ba Dokar ƙasa tace ga matakin da ake bi kafin azama, kai kuma baka bi wannan matakin ba, ka zama, to anan Kotu ce zata duba tayi hukunci” cewar Barasta.

Inda ya bada misalai da wasu Shari’u da suka gabata a shekarun baya hadda misalin Shari’ar Zamfara wadda ta kawo Gwamna Matawalle a yanzu.

Da yake fashin baƙi game da Shigar ma’aikatan Gwamnati a cikin harkokin siyasa Ɗanbaba yace Babu wata Doka da ta hana Ma’aikacin Gwamnati shiga Siyasa ko bayyana ra’ayinsa yace; ko da yake Akwai (Public Service Rules) amma wannan ba yana magana akan tauye ma Ma’aikacin Gwamnati damarsa ta Freedom of Association bane. “Ana muhimmantar da tsarin Mulki bisa ga koma wace irin Doka, idan kaga wata Doka tayi karo da kundin tsarin Mulkin ƙasa, to zaka aje waccen Dokar kabi kundin tsarin mulki.”

“Don haka Dokar ƙasa bata hana Ma’aikacin Gwamnati shiga harkokin Siyasa tsamo-tsamo ba, Sai dai da yake Najeriya ce, ana samun ƙalu bale daga ma’aikatan da su Shuwagabannin Siyasar inda da sun fahimci ba su aka goyama baya ba, bayan zaɓe sai kaga wani abu ya biyo baya maras daɗi, amma shima Doka ta baka damar garzayawa Kotu, domin a bima hakkin ka saboda abinda za’ai maka ko akai maka ya saɓa da Doka.” Inji Barasta Ahamed Ɗanbaba.

A satin nan da ya shige ne, Babban Ofishin kula da Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya wato Head of the Civil service of the Federation a turance ya fitar da wasu takardu da suke nuni da cewa bai kamata ma’aikatan Gwamnati su shiga Siyasa gadan-gadan ba. Zaku iya samun cikakkiyar Tattaunawarta ta Video a shafukan mu na yanar gizo da sauran kafafen mu na

www.katsinacitynews.com

www.taskarlabarai.com

www.thelinksnews.com

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MATSALOLIN TSARO: Gwamnatin Zamfara tabawa duk dan jiharta damar Mallakar Bindiga

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Bai Wa Ƴan Jihar Damar Mallakar Bindiga don kare kansu daga harin ƴan bindiga Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin...

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje….. Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina.

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje..... Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina. Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina...

Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi

Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam'iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi...
%d bloggers like this: