Cutar corona ta sanya Indiyawa masu bautar gumaka yin watsi da gumakan dake gidajen su saboda gaza kare gidajen nasu daga annobar cutar corona.

Indiyawa sukan saka gumakan bauta a gidajen su da zummar cewar Gunkin zai kare gida da abunda dake cikin gidan, duk da tarun gumakan dake gidajen su, gumakan sun gaza kare gidajen su daga cutar corona wacce yanzu haka take tsaka da cin kasuwar lahira a kasar ta Indiya.

Dubunan masu bautar gunki ne suka tarkata gumakan dake gidajen su zuwa ƙwandon shara sakamakon gunkin ya gaza wajen kare su daga cutar corona.

Mabanbantan Bidiyoyi sunata yawo masu nuna yadda ake ɗibar gumakan ana zubasu cikin kogi a ƙasar ta Hindu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here