Advert
Home Sashen Hausa DR MUSTAPHA ALHERI DAN KONE SOCIAL MEDIA CREW KATSINA.

DR MUSTAPHA ALHERI DAN KONE SOCIAL MEDIA CREW KATSINA.

DR MUSTAPHA ALHERI DAN KONE SOCIAL MEDIA CREW KATSINA.
————————————————————————–

Da safiyar yau talata 26/6/2021, wannan
kunkiya mai suna a sama a karkashin babban Direkta na wannan Alh Abubakar Ahmed Yantumaki tare da shugaban wannan kungiya na jiha Alh Sulaiman Garba Kafinsoli tasamu zuwa garin karamar hukumar Dutsinma gidan mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ALH ABBA JAYE Dutsinma domin neman addu’oi daga gareshi tare kara samun shawarwari da zasu taimakawa wannan kungiya wajen kara samun nasarori akan abunda tasa gaba.

Mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ALH ABBA JAYE ya nuna matukar godiyar shi a bisa ziyarar da shugabannin kungiyar suka kawo mashi domin neman tabaraki a matsayin shi na elder a karamar hukumar Dutsinma dama JIHAR KATSINA baki daya mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ALH ABBA JAYE ya kuma yabama yayan kungiyar dangane da irin yaddar suke gudanar da ayyukansu.

A lokacin da yake gabatar da jawabi ga mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA mai girma babban Direkta janar na kungiyar DR MUSTAPHA ALHERI DANKONE SOCIAL MEDIA CREW Alh Abubakar Ahmed Yantumaki akan makasudin kawoma mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ziyarar ya bayyana cewa sun kawoma mai girma SARKIN SHARIFAN wannan ziyarar duba irin yadda mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ya kasance wani babban gishiki wajen hidima ga al’ummar karamar hukumar Dutsinma dama JIHAR KATSINA baki daya.

Mai girma babban Direkta janar na kungiyar DR MUSTAPHA ALHERI DANKONE SOCIAL MEDIA CREW KATSINA ya kara da bayyana cewa wannan gida na mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA shine gidana na farko a cikin JIHAR KATSINA da wannan kungiya ta kawoma ziyarar domin neman tabaraki tare addu’oi nemam nasara a cikin tafiyar.

Alh Abubakar Ahmed Yantumaki bayyana gidan mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA a matsayin babban gida mai tarihi musanman a wajen taimakawa bayin Allah mabukata saboda haka wannan kungiya tayi duba irin ayyukan alkairin mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA yakema al’umma domin neman addu’oi daga bakinshi.

Mai girma shugaban wannan kungiya na jiha Alh Sulaiman Garba Kafinsoli yayi takaitaccen bayani akan ayyukan alkairin da kungiyar DR MUSTAPHA ALHERI DANKONE SOCIAL MEDIA CREW tayi ga al’umma dake kananan hukumumi talatin da hudu a jihar katsina da sunan mai girma sakataren gwamnatin jihar katsina DR MUSTAPHA MUHAMMED INUWA domin taimakawa matasa da mata inda ya bayyana wasu kadan daga cikin ayyukan da kungiyar tayi kama daga Free registration N-Power na mutum dubu daya da wannan kungiya tayi sai kuma bada SLOT na mutum 340 na tallafin NDE ga matasa wanda gwamnatin taraiyya ta bada tallafin kudi naira dub ashirin ashirin na tsawo wata ukku sai kuma gyare-gyaren hanyoyi tare magudanan ruwa a cikin al’umma.

Mai girma SARKIN SHARIFAN JIHAR KATSINA ALH ABBA JAYE yayi addu’oi na musanman ga wannan kungiya tare shugabanninta inda roki Allah ubangiji SWT ya sanya albarka ga kungiyar ya kuma ba wannan kungiya nasara akan ayyukanta na alkairi data sanya gaba domin taimakawa bayin Allah.

Jim kadan bayan kammala wannan zama tawagar wannan kungiya a karkashin jagoranchi babban Direkta janar na kungiyar Alh Abubakar Ahmed Yantumaki sun ziyarar babbar asibitin Dutsinma wato GENERAL HOSPITAL DUTSINMA domin duba wasu marassa lafiya da suke kwance a asibitin.

Daga tawagar wannan kungiya ta dauki hanya zuwa karamar hukumar Rimi a cikin garin tsagero domin hallartar addu’ar ukku ta babbar yayan Director Media na wannan kungiya Hon AMINU SALISU TSAGERO anyi addu’oi neman gafara ga margayiyar inda akan roki Allah ubangiji SWT yayi mata rahama yasa aljanna fiddausi ce mako a gareta.

daga nan kuma wannan kungiya ta kara samun zuwa ta’aziya a cikin garin katsina a unguwar kofar bai domin yin ta’aziya ga shugaban riko na karamar hukumar Charanci Abdulrahaman Marafa anyi addu’oi neman gafara ga margayiyar inda aka roki Allah ubangiji SWT yayi mata rahama yasa aljanna fiddausi ce mako a gareta Ameen.
Mun ciro daga shafin Facebook

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

MASARI ADVICE WEALTHY INDIVIDUALS TO INVEST ON EDUCATION.

by Ibrahim kallah Gov. Aminu Bello-Masari of Katsina State has called on wealthy individuals and groups to invest much on education through the sponsorship of...

VICTIMS OF KIDNAPPINGS IN BATSARI REGAIN FREEDOM AFTER 66 DAYS IN CAPTIVITY.

From Misbahu Batsari. Some of the victims of kidnappings were this Friday 23-07-2021 release from captivity in Batsari after spending 66 days in the hands...

Just In: Plane Crash Lands In Kwara, Passengers Evacuated

Many passengers, including some highly placed Nigerians, narrowly escaped death after an aircraft belonging to one of the major airlines crashed upon landing in...

Yar’Adua: I’ll Resist Attempt to Impose Guber Candidate on Katsina Citizens

Francis Sardauna in Katsina A chieftain of the ruling All Progressives Congress (APC) in Katsina State, Senator Abubakar Sadiq Yar’Adua, yesterday vowed to resist any...
%d bloggers like this: