Dole ne mu ya’ki ‘Kwaya ko kuma ta ya’ke mu>>>> inji Burodo

Dimokuraɗiyyar

Maiba Gwamna Shawara na musamman akan Hana Shan miyagun Kwayoyi da safarar su gami da Hana Safarar Bil’adama, Alhaji Hamza Muhammad Burodo yayi kira ga Al’ummar Jahar nan, dasu tashi tsaye domin yaki da ta’ammali da miyagun Kwayoyi, ko kuma idan akayi sake matsalar dake tattare da’ita ya shafi kowa.

Alhaji Hamza Muhammad Burodo na magantawa ne a lokacin rufe shirin horaswa na wuni guda-guda, da Sashen ya shirya ga manyan Ma’aikatan Kananan Hukumomin Jahar nan akan Matsalolin Shan miyagun Kwayoyi.

Shirin horaswar an rufe shi ne a shiyyar Katsina, wanda ya kunshi ma’aikatan Kananan Hukumomi guda 6, da suka hada da Katsina, Kaita da Jibia da Batagarawa da kuma Rimi gami da Charanchi

Alhaji Hamza Muhammad Burodo yace kwaya ce ta haddasa dukkanin Matsalolin rashin tsaro da sauran ayyukan ashsha da ake fama dasu a cikin Kasar nan, sai ya bukaci Al’umma dasu taimakawa Gwamnati wajen magance matsalar.

Ya kara dacewa Gwamnatin Jaha maici a yanzu Karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta kirkiro shirye-shiryen tallafawa da dama domin rage shan miyagun Kwayoyi da Bangar siyasa da zaman kashe wando a tsakanin matasa

Maiba Gwamna Shawara wanda ya bukaci mahalarta taron dasu maida hankali ga horaswar, yayi kira a garesu dasu shirya irin wannan horaswar tare da isar da sakon da aka sanar dasu, domin magance matsalar shan miyagun Kwayoyi.

A jawabin shi, Maiba Gwamna Shawara na musamman akan ilmi mai zurfi Dr.Bashir Usman Ruwan Godiya ya yi kira ga Al’umma dasu tabbatar sun baiwa yayensu kykkyawar tarbiyya, wanda a cewar sa hakan zai taimaka wajen rage ta’ammali da shan miyagun Kwayoyi.

A lokacin taron, Masana da suka hada da Dr.Sani Abdu Fari da Malam Muhammad Nuraddeen Umar da Sheikh Lawal Suleiman Kuraye sun gabatar da Kasidu akan Matsalolin Shan miyagun Kwayoyi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here