Advert
Home Sashen Hausa Dole Ne Mu Fara Farautar 'Yan Fashi, Mu Kashe Su Duka --El-Rufai

Dole Ne Mu Fara Farautar ‘Yan Fashi, Mu Kashe Su Duka –El-Rufai

Fulani makiyaya da suke samun dubu goma a cikin wata guda da dubu dari a shekara guda bayan sayar da saniyarsu ba za su daina fashi ba bayan suna samun miliyoyi kudi a kan aiki daya.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya yi imanin cewa hanya daya tilo da za a iya kawar da barazanar ‘yan fashi da sauran muggan laifuka a kasar nan, hanyar ita ce farauta da kashe su baki daya.

El-Rufai wanda ya kasance bako a shirin Sashen Hausa na BBC a ranar Litinin, ya ce kudurin gwamnatin Kaduna na yanzu shi ne “farautar’ yan ta’addan Fulani gwamnati ta kashe su har sai sauran sun mika wuya ko kuma su daina aikin ta’addan ci. ”

El-Rufa’i ya dage cewa kai farmaki ga yan bindigar zai nuna cewa gwamnati tana da niyyar da kuma ikon magance su.

“Wannan shine matsayin gwamnatin jihar Kaduna da takwarorinmu na Nijar.

“Mun zauna a Katsina mun yi magana da gwamnonin arewa maso gabas, wasu sun yarda da ya kamata mu shelanta yaƙi a kan yan bindigar, amma wasu na son tattaunawa da da yi musu afuwa.

Wannan ita ce matsalar da muke fuskanta.

“Kamar yadda na fada a baya, kafin yanzu, matsayin Katsina kan yan ta’addan shine tattaunawa da yin afuwa ga ‘yan bindigar amma yanzu, Katsina sun canza daga wannan matsayin suna son a shelanta cikakken yaki da ‘ yan bindigar

“Kamar yadda na kammala, Fulani makiyaya da suke samun dubu goma a cikin wata guda da dubu dari a shekara guda bayan sayar da saniyarsu ba za su daina fashi ba bayan suna samun miliyoyi kudi a kan aiki daya, Inji Shi.

“Duk wanda ya gaya muku Bafulatani makiyayi da ya yi garkuwa da mutane ya samu miliyoyin kudi zai koma salon kiwo inda yake samun dubu dari ko ɗari biyu a shekara yana yaudarar kansa.

“Don haka matsayar mu ita ce gwamnatin tarayya ta yi amfani da dukkan hukumomin tsaron ta, sojoji, sojojin sama,‘ yan sanda da dukkan jami’an tsaro don yakar su da kashe su har zuwa karshe.

“Wataƙila, idan sun fahimci cewa an rinjaye su, su ne za su zo suna roƙon afuwa.

“Ina samun rahotannin kama Fulani 10 zuwa 20 a kowace rana kuma wani yazo yana cewa za su daina, na rantse ba za su daina ba,” in ji Gwamna el-Rufai.

Dangane da batun biyan diyya da kuma yin afuwa ga ‘yan bindigar, El-Rufai ya yi watsi da irin wadannan shawarwarin.

“Meye diyya? Diyya saboda wane dalili? Waɗanda ke kashe mutane kullum, suna ƙone gidajensu, wane irin diyya suke magana? ”

Daga karshe Gwamnan ya furta hakan.

Jaridar Sokoto

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: