WANI MASANIN TSARA BURANE YA KAI rubuta korafi akan ginin shatale tale.
===Ga sakon da wasikar sa kamar yadda muka dauko a shafin sa na Facebook
Yau na mika takardar korafi ga hukumomi masu ruwa da tsaki domin su dauki matakin gaggawa na rushe ginin da ake ginawan a saman roundabout na Sabuwar tasha domin ya saba wa ka’idar raya biranai ta yanda direba bazai iya ganin ababen hawa masu shigowa daga hanyoyi ba sanadiyyar ginin ya lullube round about din. Wannan zai iya janyo karin traffic da accident. Kuma na yi kira ga hukumomi da su kira wanda yake aikin round about din domin ya sake zane wanda yayi dai dai da dokoki da tsare-tsare na birane.
Na barku lahia.
Abdulaziz.