Dokar hana Safarar Dabbobi da Dakon Man Fetur ta fara Aiki a Jihar Katsina…

Rundunar Ƴansandan Jihar Katsina tayi Nasarar kama wata Mota ƙirar kanta makare da Tumaki da Awaki sama da Tamanin 80 da ake zargin daga Dajin Zamfara suka fito a kan hanyar su ta zuwa Abuja.

Kazalika Rundunar Ƴansandan ta kuma kama wata Motar ɗauke da Mai Wanda ake zargin shima za’a kaiwa Barayin Daji ne.

Kakakin Rundunar Ƴansandan na Jihar Katsina SP Isah Gambo shine ya a gabatar da masu laifin a Shalkwatar Rundunar dake Katsina, a madadin Kwamishinan Ƴansanda CP Sanusi Buba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here