Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina na yunkurin yin dokar da zata haramta yin barace, barace a bisa tituna.

A zaman majalisar Dokoki ta Jihar Katsina na ranar Talata 29/06/2021 wanda mataimakin Kakakin Majalisar Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya jagoranta, an gabatar da kudurori guda uku.

Kudiri na farko, kudirin yin doka ne da zata haramta yin bara a bisa tituna, inda majalisar ta fara yima dokar karatu na daya, wanda shugaban masu Rinjaye na Majalisar “HOUSE LEADER” Hon. Abubakar Suleiman Abukur Korau Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rimi ya karanta.

Kudiri na biyu, kudiri ne na tantance sabon Kwamishina ma’ana Dan majalisar zartarwa na Jihar Katsina wanda Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya aika mata da sunanshi don tantance shi, watau Hon. Isah Lawal Doro, inda majalisar ta tantance shi ba tare dayi mashi wasu tambayoyi ba.

Bisaga al’ada ta majalisar idan mutum ya taba zama Dan majalisa, yazo majalisar don a tantance shi a wani mukami, majalisar tana yi mashi alfarma ya wuce ba tare da wata doguwar muhawara ba, Shidai Hon. Isah Lawal Doro ya fito ne daga karamar hukumar Bindawa, an taba zabar shi shugaban karamar hukumar Bindawa daga 1999 zuwa 2002.

Haka zalika an taba zabar Hon. Isah Lawal Doro Dan majalisar Jiha wanda ya wakilci karamar hukumar Bindawa daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2007, Hon. Isah Lawal Doro an taba zabar shi Dan majalisar Tarayya wanda ya wakilci Mani da Bindawa a majalisar wakilai ta kasa daga shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2015.

Kudiri na uku, kudiri ne da Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danmusa Hon. Aminu A. Garba ya gabatar, yana kira ga majalisar zartarwa ta Jihar Katsina data gina hanyar ruwa cikin Garin Danmusa daga bakin kasuwa, bayan tasha zuwa makabartar garin.

Da yake jawabi yayin da yake gabatar da kudirin Hon. Aminu A. Garba Danmusa ya bayyana cewa” rashin wannan hanyar ruwa ya haddasa ruwan sama lokacin damina yana shiga cikin makabartar ta garin na Danmusa yana lalata kaburburan Al’umma, wanda wannan wata barazana ce ga zamantakewarmu, wanda hakan na iya haddasa mana masifu kala, kala a bisa doron kasa.

Bayan tattauna kudirin da daukacin yan majalisar sukayi, daga karshe sun goyi bayan kudirin, yayin da Kakakin Majalisar ya umurci Kwamitin kula da kananan hukumomi da masarautu, da ya duba lamarin ya kawo rahoto yadda za’a fidda wani kaso daga cikin kudaden kananan hukumomi domin a rika kula da makabartu a Jihar Katsina.

Bayan wadannan kudurori guda uku da majalisar ta gabatar, daga karshe ta daga cigaba da zamanta zuwa gobe laraba 30/06/2021, wanda shugaban masu Rinjaye “HOUSE LEADER” na Majalisar Hon. Abubakar Suleiman Abukur Korau ya bayyana.

Rahoto
Surajo Yandaki
Edita, Mobile Media Crew
29, June 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here